Jakadan kasar Sin ya bayyana cewa, kasar tana kiran a samar da hanyar kawar da makaman nukiliya wacce a karkashinta ba za a iya raba tsaro na kashin kai da tsaro na bai daya ba, tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Babban darektan sashen kula da makamai na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Sun Xiaobo, ya shaida wa babban taron muhawara na 3 na kwamitin shirya taron koli na yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT) na shekarar 2026 cewa, kasar Sin tana nan a kan bakanta game da kin raba ‘yancin kiyaye tsaro da na sauke nauyin da ya rataya a wuyan kasashe na tsaro, da kafa shugabanci na adalci a kan hana yaduwar makaman nukiliya. Kana tana ci gaba da yin tsayin daka a kan kin raba batun tsaro da na ci gaba, tare da bai wa dukkan kasashen da abin ya shafa ‘yancin yin amfani da makamashin nukiliya ta hanyar lumana.
Sun ya yi nuni da cewa, Amurka ta yi imanin cewa, ita daidai ne a wurinta, idan ta nemi zama sawun giwa a kan sauran kasashe, da yin amfani da gwale-gwalen karin haraji da sa takunkumai, da kara matsin lamba, da kambama zalunci, da yin mummunar illa ga ka’idojin kasa da kasa, da tsarin duniya da aka tabbatar a karkashin Majalisar Dinkin Duniya, da sauran al’amura na kyakkyawan tsari da ake bi bisa dokokin kasa da kasa.
Da yake gargadi game da karuwar mamaye komai a karkashin bangare guda, da cin zarafi da siyasar nuna fin karfi kuwa, Sun ya ba da shawarar cewa, ya kamata kasashen duniya su hada kai tare da yin tsayin daka wajen nuna turjiya ga dabi’un da suka saba wa tsarin tarihi, da hana bil’adama komawa rayuwa irin ta namun daji inda masu karfi ke farautar masu rauni. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp