A jiya Alhamis 31 ga watan Yuli ne mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya yi watsi da zargin da wakilin kasar Amurka dake MDD ya yi wa kasar Sin, a yayin da ake duba batun samar wa kasar Ukraine makamai a taron kwamitin sulhu na MDD.
Geng Shuang ya ce, ba kasar Sin ce ta haifar da rikicin Ukraine ba, kana ba ruwanta da rikicin. Kasar Sin ba ta taba samar wa sassan dake rikicin munanan makamai ba. Har kullum kasar Sin tana sa ido sosai kan sayar da jirgin sama maras matuki, da sauran hajoji da fasahohi, da kuma hidimomi wadanda ake amfani da su ko dai don dalilai na jama’a ko na soja.
- Zhao Leji Ya Yi Jawabi A Babban Taron Shugabannin Majalisun Kasa Da Kasa Karo Na 6
- Sin Ta Samarwa Sassan Kasa Da Kasa Damar Shigowa Ba Tare Da Bukatar Biza Ba
Kwamitin sulhun bai sanya takunkumi kan sassan da rikicin ya shafa ba. Don haka yadda kasar Sin take gudanar da cinikayya da kasashen Rasha da Ukraine, bai saba wa dokokin kasa da kasa, da hakkokin kasa da kasa ba. Ya ce, kasar Sin ba za ta amince da danne halastattun hakkokinta ba.
Abun tambaya ma shi ne ganin cewa Amurka tana gudanar da ciniki da Rasha har zuwa yanzu, ko me ya sa take kokarin hana sauran sassan yin hakan?
Wakilin na kasar Sin ya kara da cewa, yayin da Amurka ke fatan kasar Sin ta taka rawa ganin wajen kawo karshen rikicin, a daya hannun tana kara matsa wa kasar Sin lamba tare da shafa mata kashin kaji.
Kasar Sin ta sake neman Amurka, da ta daina zarginta, da dora mata laifi, ya kamata kasar Amurka ta taka rawa wajen tsagaita bude wuta, da kara azama ga gudanar da shawarwarin shimfida zaman lafiya. Jami’in ya ce, ana bukatar hadin kai wajen warware rikicin Ukraine, a maimakon rarrabuwar kawuna da yin fito-na-fito. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp