An bude taron baje kolin cinikayya da zuba jari na duniya karo na 25 a birnin Xiamen na lardin Fujian na kasar Sin, a jiya Litinin.
Hakika baje kolin cinikayya da zuba jari babban jigo ne ga habakar tattalin arzikin duniya bisa la’akari da kyakkyawan tasirinsa da yadda yake samar da wani cikakken dandali da ya hada bangarori da dama daga gwamnatoci da ’yan kasuwa zuwa dukkan masu ruwa da tsaki.
- Nijeriya Ta Rasa Tikitin Kai Tsaye Na Zuwa Gasar Kofin Duniya
- Tarihi: Mugunta Ba Za Ta Iya Lashe Adalci Ba
Yayin da duniya ke shiga sabon zamani na cudanyar bangarori daban-daban da rarrabuwar iko tsakanin kasashe maimakon kasancewa karkashin ikon wasu ’yan tsiraru, hanyar ganin dorewar hakan ita ce hadin gwiwa da bude kofa da cin moriyar juna.
Sabanin yadda wasu kasashe ke tayar da takaddamar cinikayya da kawo cikas ga ci gaban tattalin arziki da tsarin samar da kayayyaki a duniya, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen ganin duniya ta samu ci gaba, musammam kasashe masu tasowa, ta hanyar bude kofa da yin komai cikin adalci.
A duk inda aka ambaci “Babba”, to a ko da yaushe, shi ne mai nuna sanin ya kamata da tallafawa da jagorantar na kasa, domin su zamo masu dogaro da kan su da bin daidaitacciyar hanya. Wannan kuma ya yi daidai da dabaru da manufofin kasar Sin, inda take mayar da hankali kan yadda za a gudu tare a tsira tare tsakaninta da kasashe masu tasowa.
A sakonsa na murnar bude baje kolin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nanata cewa, kasarsa za ta fadada bude kofa domin kara kuzari da tabbaci ga ci gaban duniya. Bude kofar kasar Sin ba dama ce kawai ga kasashe su shigo su ci gajiyar babbar kasuwarta ba, ya kara bayar da dama tare da zama dandalin da kasa da kasa za su hadu, su kulla huldar cinikayya da zuba jari.
Baje kolin cinikayya da zuba jari, yana kawo nesa kusa, wato yana saukakawa da dunkule hanyoyi masu sarkakiya kamar na binciken kasuwa, haduwar ’yan kasuwa da tattaunawa a wuri guda, lamarin dake kara fa’ida da daraja ga kasashe da kayayyaki da masana’antu da fadada hanyoyin kasuwanci har ma da rage kudin da ake kashewa. Ke nan, irin wannan bude kofa da Sin ke kara fadada aiwatarwa kasashen duniya suke bukata domin tsayawa da kafarsu da inganta cudanya a tsakaninsu, ta yadda za a kai ga dunkule tattalin arzikin duniya da wanzar da zaman lafiya a tsakaninsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp