Gwamnatin kasar Amurka ta yanzu, ta gaji matakan da tsohuwar gwamnatin kasar ta aiwatar, inda ta ce za ta ci gaba da haramtawa Amurkawa zuba jari ga kamfanonin kasar Sin masu alaka da aikin soja.
Hakan a cewar mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya gamu da babbar adawa daga gwamnatin Sin.
Zhao ya ce, gwamnatin Amurka ta yanzu ta ci gaba da aiwatar da matakan da tsohuwar gwamnatin kasar ta yi, na sanya haramci kan zuba jari ga kamfanonin kasar Sin “masu alaka da aikin soja”, domin cimma muradun siyasa, wanda hakan tamkar yin biris ne da gaskiya, da watsi da hakikanin halin da kamfanonin suke ciki, da illata ka’idojin kasuwanni, wanda kuma ake kallo a matsayin illa ga moriyar kamfanonin kasar Sin, har ma da moriyar masu zuba jari na kasa da kasa, ciki har da na Amurka.
A dayan bangaren kuma, game da zaben tsakiyar wa’adin Amurka, Zhao ya bayyana a yau Laraba cewa, abu ne da ya shafi harkokin gidan Amurka, kana, masu kada kuri’un kasar ne za su yanke hukunci. Ya ce kasar Sin ba za ta yi wani sharhi ba.
Zhao yana kuma fatan Amurka za ta hada kai tare da kasar Sin, wajen neman hanya madaidaiciya ta kyautata dangantaka tare da kasar Sin a sabon zamaninmu, a wani kokari na raya huldodin kasashen biyu ta hanyar da ta dace. (Murtala Zhang)