A jiya Laraba 3 ga wata, kasar Sin ta gudanar da kasaitaccen bikin faretin soja a birnin Beijing, don tunawa da cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da ma yakin duniya da tafarkin murdiya, bikin da ya jawo hankalin duniya, har ma wasu abokaina ‘yan Nijeriya sun turo min sakonni, inda suka ce su ma sun kalli gaba dayan bikin, kuma suna mai jinjinawa ga kasar Sin, musamman ganin yadda ta bunkasa har ta zama kasa mai karfin tattalin arziki ta biyu a duniya, bayan yadda ta kasance kasar da aka kai mata hari tare da mamaya a baya. A wata makala da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya wallafa a shafinsa, ya yi nuni da cewa, kwarin gwiwar da jama’ar kasar Sin suka samu daga yaki da maharan kasar Japan ya zama arziki gare su, wanda ya ke matsa musu kaimin tinkarar matsalolin da wahalhalun da ke gabansu, don cimma burin zamanantar da kasarsu da farfado da al’ummun kasar.
Na kuma lura da cewa, shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da shugaban jamhuriyar Congo Denis Sassou Nguesso sun zo kasar Sin don halartar bikin. Kafin ya tashi zuwa kasar Sin, shugaba Sassou ya bayyana cewa, nasarar yakin duniya da tafarkin murdiya ta dogara ne da kokarin da dukkanin al’ummomin duniya masu kishin zaman lafiya da adalci suka yi, idan har masu bin tafarkin murdiya suka cimma nasarar yakin a lokacin, lallai da wuya mu yi zaton irin duhun da dan Adam zai shiga. Ya ce, al’ummar kasar Sin sun bayar da muhimmiyar gudummawa ga cimma nasarar yakin, a yayin da al’ummun kasashen Afirka da dama ma suka sadaukar da rayukansu a yakin, wadanda suka ketare hamadar Sahara da Bahar Rum, suka shiga yakin kafada da kafada tare sojojin kasashen kawance. Abin haka yake, yakin da aka yi da tafarkin murdiya a shekaru 80 da suka wuce, ya kasance turjiyar al’ummomin kasashen duniya, ciki har da na kasar Sin da kasashen Afirka, ga hari da zaluncin mulkin danniya, wanda hakan ya zama nasarar masu kishin adalci da zaman lafiya.
A ganina, dalilin da ya sa bikin tunawa da nasarar da kasar Sin ta shirya ya burge bangarori daban daban na kasashen Afirka, shi ne sabo da abubuwa kusan iri daya ne suka faru a gare su a tarihi, wato dukkansu sun taba fuskantar mamayar mahara da ma mulkin mallaka da aka yi musu, kuma suka samu ‘yancin kansu bisa ga fafatawar da suka yi, har wa yau kuma, dukkansu suna da burin tabbatar da ci gabansu da ma farfado da al’ummunsu. Sakamakon hakan kuma, sun fi fahimta da kishin zaman lafiya da ci gaba.
Sai dai ko da yake tuni zaman lafiya da ci gaba sun zama jigon zamanin da muke ciki, amma har yanzu akwai rina a kaba, inda ake ta kara fuskantar matsalolin daukar matakai na kashin kai da kariyar ciniki da nuna fin karfi a duniya, kuma zaman lafiya ko yaki, yin shawarwari da juna ko yin fito na fito da juna, cin moriyar juna ko cin nasara daga faduwar wani bangare, ya zama sabon zabi ga dan Adam. Kamar yadda Bahaushe kan ce, waiwaye adon tafiya, kasar Sin ta shirya bikin tunawa a daidai wannan lokaci, ba don neman ci gaba da kiyayya da juna ba, a maimakon hakan, tana son kira ga al’ummomin duniya da su tsaya tsayin daka a kan kiyaye zaman lafiya da magance yaki a tsakaninsu.
A lokacin kawo karshen bikin faretin da aka yi, tantabaru kimanin dubu 80 ne suka tashi, wadanda suke dauke da sakon fatan alheri na al’ummar Sinawa game da tabbatar da zaman lafiya a duniya. Tabbas kasar Sin za ta nace ga bin hanyar tabbatar da ci gabanta cikin lumana, kuma za ta hada karfi da karfe da al’ummomin duniya, ciki har da na kasashen Afirka, wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkanin bil’adama, don ba da gudummawarta wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba na dindindin a fadin duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp