Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar 17 ga wata, rundunar ‘yan sandan Uganda ta bayyana cewa, dakarun da ke adawa da gwamnatin kasar (ADF) sun kai hari wata makaranta a Uganda a ranar 16 ga wata, inda suka kashe mutane 41. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a gun taron manema labaru da aka saba gudanarwa a yau Litinin cewa, kasar Sin ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren da aka kai wa fararen hula, musamman ma dalibai, inda ta mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma jajantawa wadanda suka jikkata.
Baya ga haka, Mao Ning ta jaddada cewa, kasar Sin tana adawa da duk wani nau’in tashin hankali da ta’addanci, kuma za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kokarin Uganda na tabbatar da tsaron kasa da zaman lafiyar al’umma. (Mai fassara: Bilkisu Xin)