Kasar Sin ta gabatar da daftarin ka’idojin gina ababen more rayuwa na bayanai na kasar, ciki har da habaka tsarin sadarwa na 5G zuwa matsayin 5G-A, da sa kaimi ga bincike, bunkasa da kirkire-kirkiren da suka shafi fasahar sadarwa ta 6G.
Hakazalika, kasar Sin za ta daidaita aikin samar da hanyoyin sadarwa na kasa da kasa a yankunanta na gabas, tsakiya da kuma yammacin kasar, tare da fadada wayoyin sadarwa na kasa da kasa na karkashin ruwa da na doron kasa. Za kuma a samar da intanet na tauraron dan Adam wanda zai hada ababen more rayuwa n sararin samaniya da na doron kasa, a cewar takardar da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar a ranar Juma’a. (Mohammed Yahaya)