Hukumar kwastam ta kasar Sin ta bayyana cikin wata sanarwa Jumma’ar nan cewa, daga ranar 1 ga watan Maris na wannan shekara, kasar Sin za ta soke haraji kan nau’o’in hajjoji da yawansu ya kai kashi 98 cikin 100 wadanda ake shigowa daga kasashen Habasha,da Burundi da Jamhuriyar Nijar.
A cewar hukumar, sabon matakin zai samar da ruhin abokantaka da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da taimakawa kasashe mafiya karamin karfi wajen bunkasa ci gabansu, da kara bude kofa ga kasashen duniya.
Ta kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da fadada irin wannan gatanci sannu a hankali zuwa ga dukkan kasashe mafiya karamin karfi da suka kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin. (Ibrahim)