Firaministan kasar Sin mista Li Keqiang ya ce, tattalin arzikin kasarsa ya hade da na duniya cikin wani matsayi mai zurfi, kana bude kofarta ga duniya wata babbar manufa ce ta kasar.
Saboda haka, Sin za ta tsaya kan wannan muhimmiyar manufa, gami da kokarin inganta harkoki a wannan fanni.
- Wani Dan Kasuwan Kasar Sin Ya Bullo Da Shirin Magance Matsalar Gurbataccen Ruwa Sha A Nahiyar Afirka
Mista Li ya fadi haka ne a jiya Talata, yayin da yake halartar taron manyan ‘yan kasuwan kasashe daban daban karkashin laimar dandalin tattauna tattalin arzikin duniya, wanda ya gudana ta kafar bidiyo.
A cewar firaministan kasar Sin, manufar bude kofar kasar ta shafi kasashe masu sukuni, da wadanda ke kan hanyar tasowa.
Sa’an nan kasar Sin za ta ci gaba da kokarin kare tsarin ciniki da ya shafi bangarori daban daban, da kungiyar ciniki ta duniya WTO take jagoranta, da sa kaimi ga yin ciniki cikin ‘yanci da adalci.
Firaminista Li ya kara da cewa, kasarsa za ta kara kokarin daidaita muhallin gudanar da harkokin kasuwanci, da daukar matakan kandagarkin annobar COVID-19 masu dacewa, da kyautata yanayin ayyukan samar da izinin shiga kasar, da gudanar da gwajin kwayoyin cutar COVID-19. Haka kuma za ta taimakawa mutanen da suke neman yin ciniki ko aiki a kasashen ketare, don inganta mu’ammalar jama’ar Sin da ta kasashen waje.
Ban da wannan kuma, babban jami’in ya nanata cewa, kasar Sin za ta kiyaye manyan manufofinta na yanzu, don tabbatar da cimma burinta na raya tattalin arziki zuwa wani matsayin da take bukata, a wannan shekarar da muke ciki. Ya ce, sabon zagayen yaduwar cutar COVID-19 a duniya gami da sauran abubuwan da ba a iya hasashensu ba, sun sa tattalin arzikin Sin fuskantar matsi.
Duk da haka, a cewar firaministan, matakan daidaita yanayin da gwamnatin kasar Sin ta dauka, musamman ma wadanda suka shafi ba da tallafi ga kamfanoni, da shawo kan hauhawar farashin kayayyaki, sun yi amfani, inda suka sanya tattalin arzikin kasar komawa yanayi na karuwa, sai dai kuma ana bukatar daukar karin matakai don tabbatar da dorewar yanayin. (Bello Wang)