Tsarin shigo da kaya Nijeriya daga kasashen waje ya bayar da damar a shigo da kaya da dama da ba a dasu a cikin gida, kayayyakin sun hada da na kimiyya da fasaha da kuma kayayyakin amfanin yau da kullum. Wadannan kayayyakin suna taimakawa wajen bunkasar tattalin arzikin kasa ta hanyar tallafa wa ayyukan masana’antu daban daban, don ganin suna tafiya yadda ya kamata.
An dade ana tattauanwa a kan wannan lamarin inda wasu masana ke ganin ba yadda tattalin arzkin kasa zai bunkasa ba tare da ana shigo da kaya daga kasashen waje, yayin da kuma wasu ke ganin Nijeriya na shigo da wasu kayyakin da za a iya sarrafa su a cikin gida.
- Sin Na Taka Rawar Gani Wajen Raba Fasahohinta Na Bunkasa Tattalin Arziki Na Zamani Da Sauran Kasashe Masu Tasowa
- Azabtar Da ‘Yar Shekaru 12 Da Wuta: Gwamnatin Zamfara Ta Nemi A Hukunta Wacce Ake Zargi
Duk da haka ya kamata a fahimci cewa, kasancewar Nijeriya babar kasa kuma babar kasuwa ya zama dole a samar da kayayyakin da al’ummar kasa za su yi amfani da su don harkokin su na kullum in ba haka ba kuma al’umma za su wahala za kuma a shiga matsala.
Ganin yawan al’ummar Nijeriya, kamar yadda muka yi bayani a baya, dole kayayyakin da Nijeria ke shigowa dasu su fi na sauran kasashen Afirika. Musamman in aka lura da kayayyakin da aka shigo da su a wannan zango na 3 na wannan shekarar 2023.
Hukumar kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce, kayayyakin da Nijeriya ta shigo da su a zango na 3 na wannan shekarar 2023 ya kai na Naira Biliyan 8,457.68 wanda ya kama kashi 47.70 in aka kwatanta da abin da aka shigo dasu a zango na 2 na (₦5,726.25 biliyan) hakan ya nuna karuwa da kashi 33.33 in aka kwatanta da abin da aka shigo da shi a zango na biyu na shekarar 2022 na (₦6,343.53 biliyan).” A wannan zangon, Nijeriya ta shigo da kaya kala kala tun daga abin da ya shafi kayan sarrafawa a masana’antu dana amfanin yau da kullum.
Kasashen da Nijeriya ta fi shigo da kaya sun hada da Chana inta da shigo da kashi 23.33, (Naira biliyan 1,973.34), Belgium kuma kashi 11.78 inda aka shigo kayan Naira biliyan 996.65, Indiya kashi 9.48 an shigo da kayan Naira biliyan 802.07 sai kasar Malta dake da kashi 6.64, an shigo da kayan Naira biliyan 561.37 sai kuma kasar Amurka inda aka samu kashi 5.95 wanda ya yi daidai da Naira Biliyan 502.92.