Kungiyar nan ta kasa da kasa, ta Global Firepower, mai fitar da jadawalin mizanin karfin sojojin kasashen duniya, ta fitar da rahoton da ke cewa a shekara ta 2025 Nijeriya ta kasance ta 39 a karfin soji daga cikin kasashe 145 na duniya.
Shekaru uku jere karfin sojojin kasar na raguwa kamar yadda rahoton kungiyar ya nuna.
- Ayyukan Jami’an Ilimi Da Muhimmancinsu (3)
- Za Mu Farfaɗo Da Masana’antun Dinki 44 Da Aka Yi Watsi Da Su – Gwamnatin Kano
A duniya, Amurka ce ta farko a jadawalin inda ta shafe shekaru 18 jere tana kan matsayin.
Sauran kasashen da suke baza karfin sojinsu sun hada da Rasha, da China, da Indiya, da kuma Koriya ta Kudu wadda ta kasance kasa ta biyar a duniya da take da karfin soji.
Mun yi nazarin jadawalin da kungiyar ta fitar ga kuma jerin kasashe biyar da suka fi karfin soji a nahiyar Afirka.
Masar
Masar ce kasa ta farko a nahiyar Afirka kuma ta 19 cikin kasashe 145 na duniya da kungiyar ta yi nazarin karfin sojinsu a 2024.
Kungiyar ta GFP ta bayyana cewa Masar tana bajekolin kokarin da take na zamanantar da tsarin tsaronta inda take da dubban motocin sulke da sauran makaman yaki.
Masar ta rike wannan matsayi ne saboda yadda take iya kera manyan makamai na fasaha, da yawan ma’aikatanta, da karfin sojin ruwanta, da na jiragen sama na musamman, da kuma kasafin tsaro mai yawa.
Shugaba Abdel Fattah El-Sisi ya bayar da gudummawa wajen samar da gagarumin ci gaba a fannin karfin soji da sabunta makaman kasar. Kasar ta kulla alaka mai karfi da kasashen duniya wajen habaka dakarun kasar.
yawan sojojin Masar sun kai dubu dari hudu da arba’in yayin da take da jiragen yaki 238.
Masar na kashe kusan dala biliyan shida duk shekara a harkokinta na tsaro, kamar yadda nazarin GFP ya bayyana.
Aljeriya
Aljeriya ce ta biyu bayan Masar wajen karfin soji a nahiyar Afirka inda kuma a jerin kasashen duniya ta kasance ta 25.
Kamar kowace kasa, Aljeriya tana da sojoji na kasa na ruwa da kuma na sama kari da dakarun tsaron sararin samaniya wadda ta maye gurbin sojin National Liberation Army, wani bangare na kungiyar National Liberation Front da ta yi yaki da mulkin mallakar Faransa lokacin yakin nemar wa Aljeriya ‘yancin gashin kai tsakanin shekarar 1954 zuwa 1962.
Kungiyar ta GFP ta kiyasta cewa kasafin da kasar ke ware wa bangaren tsaronta duk shekara ya kai Dala biliyan 25.
Tana kuma da jiragen yaki 102 da sojoji dubu dari uku da ashirin da biyar.
Nijeriya
Nijeriya ce ta uku a Afirka, kuma ta 31 a duniya cikin kasashe 145 inda ta samu maki 0.5771.
Nijeriya tana bayar da gudummawa sosai wajen samar da tsaro a yammacin Afirka saboda kasafin kudin da take ware wa tsaro da kuma ayyukan sabunta makaman yaki.
A cikin gida kuma, dakarun kasar na bayar da gudummawa wajen murkushe ayyukan ta’addanci musamman a yankin arewa maso gabas sannan kuma ta kasance daya daga cikin na gaba-gaba a Afirka da ke kokarin wanzar da zaman lafiya a duk lokacin da aka samu barkewar hatsaniya a wata kasa ta nahiyar.
A kasafin kudin da gwamnatin kasar ta ware wa bangaren tsaron ya kai naira tiriliyan 4.91, fiye da adadin da aka ware wa bangaren a kasafin da ya gabata.
A jadawalin GFP, Nijeriya tana ware sama da dala biliyan uku a jumulla wajen tafiyar da al’amuran tsaron kasar duk shekara.
Tana kuma da jirage yaki 14 sannan yawan sojojinta sun kai 230,000.
Afirka ta Kudu
Afirka ta Kudu ce kasar da ke biyewa Nijeriya inda ta zo ta hudu a Afirka kuma ta 40 a duniya.
Afirka ta Kudu ta yi fice wajen amfani da makamai na zamani da kwararrun sojoji saboda albarkatun kasar da take da su.
Kasa ce da ta fifita tsaronta sannan kuma tana shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasashen da aka samu tarzoma.
GFP ta bayyana cewa kasar tana ware dala biliyan 2,266,800,000 a matsayin kudin ta take kashewa a bangaren tsaronta.
Sannan kuma tana da yawan sojojin da suka kai 71, 235 hadi da jiragen yaki biyu.
Habasha
Habasha ta kasance ta biyar a Afirka kuma ta 52 a duniya a karfin soji
Kungiyar ta GFP ta bayyana cewa Habasha ta ware sama da dala biliyan biyu don tafiyar da harkokin tsaron kasar.
A cewar jadawalin, kasar tana da yawan jiragen yaki da suka kai 25 sannan yawan sojojinta sun kai dubu dari da sittin da biyu.