Kungiyar kasashen Larabawa wato AL, ta amince da maida Syria mamba a kungiyar a ranar Lahadi 7 ga watan nan, bayan da aka mayar da ita saniyar ware na tsawon shekaru 12 da suka gabata. Ana dai ganin cewa, wannan sabon ci gaba ne da aka samu, a yunkurin sulhuntawa a yankin na Gabas ta Tsakiya, bayan da kasashen Saudiyya da Iran suka daddale yarjejeniyar sulhuntawa a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin a watan Maris da ya wuce.
Yawancin kasashen duniya sun yi maraba da kudurin maida Syria mambar kungiyar ta AL, yayin taron ministocin harkokin wajen kungiyar da aka kira. Kaza lika wasu masana harkokin kasa da kasa na ganin cewa, matakin da aka dauka zai amfani kasar Syria, a kokarin ta na kara karfafa hadin gwiwa da sauran kasashen shiyyar, da kyautata tattalin arziki, da kuma sake gina kasar bayan yaki, baya ga karfafa tasirin siyasar kungiyar ta AL a duniya, gami da kasashen Larabawa baki daya. Haka kuma, matakin zai taka rawar gani wajen daidaita rikicin Syria a siyasance, tare kuma da ingiza kyautatuwar yanayin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki.
Hakika kasar Amurka ta rika daukar matakai kan kasashen yankin Gabas ta tsakiya a cikin ‘yan watannin da suka gabata, saboda bijirewar su ga yunkurin na ta, kuma Amurka ba ta cimma burinta na dakatar da sulhuntawa a yankin ba, inda kasashen yankin suka tabbatar da burikansu na wanzar da zaman lafiya, da samun ci gaba ta hanyar da suka zaba. (Mai fassarawa: Jamila)