• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasashen Sin Da Afghanistan Da Pakistan Sun Sha Alwashin Karfafa Hadin Gwiwar Inganta Tsaro

by CMG Hausa
3 years ago
Afghanistan

LABARAI MASU NASABA

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

Kasashen Sin da Afghanistan da Pakistan, sun bayyana aniyar su ta karfafa hadin gwiwa a fannin tabbatar da tsaro, da yaki da ayyukan ta’adanci.

Kusoshin kasashen da suka hada da ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, da takwaransa na Pakistan Bilawal Bhutto Zardari, da mukaddashin ministan harkokin wajen gwamnatin rikon kwarya ta Afghanistan Amir Khan Muttaqi, su ne suka bayyana hakan a ranar Asabar, yayin taron da suka gudanar a birnin Islamabad, fadar mulkin Pakistan.

Yayin da yake tsokaci game da wannan aniya ta kasashen uku, dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Qin Gang, ya ce kasar sa a shirye take ta raba damammakin ta na ci gaba da sauran sassan 2, da sauke nauyin dake wuyan ta na shawo kan kalubalen tsaro tare da kasashen 2, kana tana fatan samar da wani kyakkyawan misali na hadin gwiwar makwaftaka tare da kasashen 2, da kyautata cudanyar rukunin su, da mayar da hankali ga muhimman batutuwan dake jan hankalin su, karkashin kawancen kasashe biyu-biyu, da kuma na jimillar kasashen 3.

Qin ya kara da cewa, bangaren kasar Sin zai shiga hadin gwiwar wanzar da tsaro da yaki da ta’addanci tare da Afghanistan da Pakistan, zai kuma martaba manufar su ta bai daya, karkashin cikakken tarin hadin gwiwa da tsaro mai dorewa, kuma Sin din za ta kalubalanci duk wani nau’in ta’addanci, da raba kafa a manufofin yaki da ta’addanci.
A nasu bangaren kuwa, Muttaqi da Bilawal, sun bayyana cewa, hadin gwiwa tsakanin Sin da Afghanistan da Pakistan, na da matukar muhimmanci a fannin wanzar da tsaro da wadata a yankin su. Sun kuma sha alwashin shiga a dama da su wajen ingiza hadin gwiwar su tare da Sin, tare da samar da wani managarcin tsari na fadada hadin kai a fannonin siyasa, da tsaro da raya tattalin arziki, kana da kare moriyar kasashen 3, ta yadda za su cimma moriyar juna, da samarwa al’ummun kasashen 3 makwaftan juna, da ma na sauran kasashen yankin su alherai masu dimbin yawa. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

November 7, 2025
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka
Daga Birnin Sin

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

November 7, 2025
Next Post
Bincike Ya Gano Yi Wa Mata Jima’i Ta Baki Ya Fi Shan Taba Da Giya Hadari

Bincike Ya Gano Yi Wa Mata Jima’i Ta Baki Ya Fi Shan Taba Da Giya Hadari

LABARAI MASU NASABA

An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi

An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi

November 8, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

November 7, 2025
Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

November 7, 2025
Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

November 7, 2025
An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025
Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

November 7, 2025
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

November 7, 2025
APC Da Uba Sani Ba Su Lashe Zaben Gwamnan Kaduna Ba -PDP

Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna

November 7, 2025
Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.