Jami’in Kwastan, Hamza Abdullahi Elenwo, ya rasa ransa yayin wani aikin bincike a jiya Juma’a, 12 ga Yuli, 2024, a Aci Lafiya a kan hanyar Daura-Kano a Jihar Jigawa. Hukumar Kwastan ta ƙas, Aiyukan da suka shifi tarayya (FOU), shiyyar B, ta tabbatar da faruwar wannan lamarin a cikin wata sanarwa da Kakakin Hukumar, Sifritanda Isah Suleiman, ya fitar.
Wannan mummunan al’amari dai ya faru ne yayin da wata mota da ake zargin an shigo da ita cikin ƙasa ba bisa ƙa’ida ba, ta buge Elenwo a yayin da Direban yake kokarin gujewa kamun. An garzaya da Elenwo zuwa Asibitin Kazaure sannan aka wuce da shi zuwa Cibiyar kula da Lafiya ta Tarayya (FMC) Katsina, inda acan aka tabbatar da mutuwarsa.
- Hukumar Kwastam Ta Yi Gwanjon Litar Man Fetur 25,162 Ga Jama’a A Sokoto
- Yadda Amurka Ta Yi Kokarin Amfani Da Nukiliya Wajen Tarwatsa Wata
Marigayin ɗan asalin Fatakwal, Jihar Ribas ne, kuma ya shiga aikin Kwastam ta Nijeriya a shekarar 2013, an kuma ɗaukaka shi zuwa mukamin Sufeto a shekarar 2022. Ya bar matarsa da ‘ya’ya biyu.
Kwanturolan Aiyukan da suka shifi tarayya (FOU), shiyyar B, Ahmadu Shuaibu, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Elenwo tare da yin Allah wadai da irin halayen wasu Direbobin da masu fasa kwauri ke yi don tsira daga kamu. Ya tabbatar da cewa wani wanda ake zargi yana hannun ‘yan sanda a halin yanzu.