Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya (EFCC), ta bayyana cewar kiyasin kaso 70 cikin dari na laifukan da suka shafi babakere da handamar kudade a fadin Nijeriya na da alaka da bankuna.
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, shi ya bayyana hakan a lokacin da ke jawabi a Abuja a wajen babban taron kungiyar masu manyan binciken kudade na bankuna a Nijeriya.
- An Dakatar Da Bellingham Daga Buga Wasanni Biyu Na Laliga Sakamakon Rikici Da Alkalin Wasa
- An Yanka Ta Tashi: Jami’ar Modibbo Adama Ta Kori Dalibi, Ministan Ilimi Ya Ce Bai Koru Ba
Shugaban EFCC ya kara da cewa, ‘yan damfara na kara amfani da bankuna sosai, lamarin da a cewarsa ya kara ninka wa hukumar kalubalen da take buga-bugar yaki da su.
Olukoyede, wanda ya samu wakilcin daraktan bin diddigin kudade na hukumar, Idowu Apejoye, ya jaddada muhimmancin da ke akwai na yin aikin hadin guiwa a tsakanin hukumomin da suke da ruwa da tsaki, kamfanonin kwararru, daidaikun mutane da kuma shugabannin rassan da ke da alaka da hada-hadar kudade, domin ganin an tunkari matsalar gami da dakile aniyar masu damfara a bangaren hada-hadar kudade.
“Balo-balo nake magana, zamba a ciki da wajen Nijeriya na da alaka da bankuna. Zamba da ake samu a cikin bankuna sun kunshi sayar da shaidar ajiye kudi na kwastomomi wato deposits, samar da yanayin lamunin bashi, amfani da takardun bogi da sauran bangarorin da ake amfani da su wajen aikata zamba.
“Zambar waje kuma sun hada da kutse wajen shiga asusun mutane, damfarar katin cire kudi ATM, rashawa, da sauran dangoginta. Amma, tare da hadin guiwa a tsakaninmu dukka, za mu iya kawo karshen wadannan matsalolin.