ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kashi 70 Na Fursunonin Nijeriya Ba A Yanke Musu Hukunci Ba

by Sani Anwar and Sulaiman
5 months ago
Daurarru

Biyo bayan rahoton baya-bayan nan, game da fursunoni 86,000 a Nijeriya, babban jami’in gudanarwa na kamfanin Moneda, wani kamfanin hada-hadar kudi, Ejike Egbuagu, ya kaddamar da gidauniyar Egbuagu, da nufin ‘yantar da fursunoni 1,000 da ake tsare da su; ba bisa ka’ida ba a dukkanin fadin Nijeriya.

Kaddamar da bikin, wanda ya yi daidai da cikar Egbuagu shekaru 40 da haihuwa, ya gudana ne a gidan Moneda da Lekki a Jihar Legas, wanda ya samu halartar kwararrun masana shari’a da dama da suka yi alkawarin tallafa wa wannan gidauniya.

  • Ribadu Ya Kara Jaddada Gargadinsa Kan Biyan Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane
  • Kasar Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Mai Samar Da Sadarwar Intanet

Har zuwa ranar 28 ga watan Afrilun 2025, gidajen yarin Nijeriya na amfani da kashi 136.7 cikin 100, wanda ke nuni da cewa; akwai matukar cunkoso a wadannan gidaje na yari. Jimillar wadannan fursunoni, sun hada da wadanda aka yankewa hukunci da kuma wadanda ake tsare da su kafin yanke musu hukuncin.

ADVERTISEMENT

Bisa kididdigar baya-bayan nan da hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Nijeriya ta yi da kuma rahotanni daga kungiyoyin kare hakkunan shari’a, kashi 70 cikin 100 na fursunonin da ke gidajen yarin Nijeriya, na nan suna dakon shari’a, ma’ana ba a yanke musu hukunci ba. Yayin da kimanin yara 26,000, ke gidan yari ko kadai iyayensu sun haife su a can ko kuma ana tsare da su ba tare an tabbatar da laifin da suka aikata ba.

Da yake yin jawabi a wajen kaddamar da taron, Egbuagu ya bayyana cewa; gidauniyar ta fara mayar da hankali ne wajen kyautata jin dadin fursunonin tare kuma da kokarin ganin an sako wadanda ake tsare da su, ba bisa ka’ida ba.

LABARAI MASU NASABA

Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai 

Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC

“Gidauniyarmu ta farko da aka kafa a shekarar 1952, ta tallafa wa masu fasaha daban-daban na Afirka, ta hanyar ba su damar shiga kasuwannin duniya. Gidauniyar Egbuagu, wadda aka kaddamar a yau; za ta mayar da hankali ne wajen kula da ayyukan shari’a, domin taimaka wa ‘yan Nijeriyan da ake tsare da su ba bisa ka’ida ba,” in ji shi.

“Babban bangaren da za mu bai wa fifiko shi ne, na matasan fursunoni, masu basirar kirkire-kirkire. Muna so mu taimaka musu su yi amfani da kwarewarsu, domin samun damar rike kawunansu ko da kuwa a gidajen yarin ne. Kazalika, bincikenmu zai mayar da hankali kan shekaru da kuma yanayin daurin da aka yi musu.”

Dangane da batun hadin gwiwa kuwa, Egbuagu ya kara da cewa; “Mun shirya yin aiki tare da kungiyoyin lauyoyi, ciki har da masu yin aiki kyauta. Tuni dai, wasu daga cikin kamfanonin lauyoyi da dama suka yi alkawarin taimaka mana, yayin da wasu lauyoyin kuma suka sha alwashin yin aiki da mu kyauta, a wasu lokutan kuma za mu biya su; idan akwai bukatar hakan.

Ya kara da cewa, ‘yan Nijeriya su yi tsammanin fara cikakken wannan aiki na gidauniya nan da watan Yunin 2025.

“A yanzu haka, muna kokarin kammala yarjejeniya tare da abokan aikinmu tare kuma da gabatar da kawunanmu ga gidajen fursunonin da ayyana abubuwan da muke son aiwatarwa. Mafi yawan wadannan fursunoni, ba su da ko da fayel, don haka; a cikin tsarikan da muke da su, za mu samar musu da fayal-fayal tare kuma da rubuta dalilan da yasa bai kamata su ci gaba da kasancewa a wadannan wurare ba.

“Wannan aiki, ko shakka babu zai dauki kimanin kwana 90, bayan haka; za mu fara shiga tsakani tare kuma da sanar da kamfanoni masu zaman kansu.”

Wata babbar lauya, mai suna Zikora Okwor-Wewan, wadda ita ma ta halacci kaddamarwar, ta bayyana farin cikinta game da wannan shiri, “Na yi aiki da fursunonin da ke jiran shari’a da kuma wadanda aka daure a gidajen yari ba bisa ka’ida ba. Lokacin da na ji batun wannan gidauniya, na yi matukar murna tare da yanke shawarar kasancewa tare da ita. Haka zalika, taimakawa wajen ‘yantar da fursunoni kimanin 1,000, na daya daga cikin ayyukan da nake so tare kuma da sha’awar yi”, in ji ta.

Har ila yau, ya sake nanata wannan kididdiga: “Nijeriya na da fursunoni kimanin 80,000, amma kusan kashi 70 cikin 100, har yanzu suna nan suna jiran shari’a. Kazalika, kusan kimanin 26,000 daga cikinsu, kananan yara ne, wadanda ko dai wadanda aka kama ko kuma wadanda aka haifa a can. Wasunsu ma, ba su da ko da shaidar takardun haihuwa, wasu kuma sun makale ne kawai a cikin tsarin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai 

November 17, 2025
Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC
Manyan Labarai

Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC

November 17, 2025
Tsohuwar Firaministan Bangaladesh Sheikha Hasina,
Kasashen Ketare

An Yanke Wa Tsohuwar Shugabar Bangladesh Hukuncin Kisa

November 17, 2025
Next Post
Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Wajen Inganta Amfani Da Ruwa A Shekarar 2024

Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Wajen Inganta Amfani Da Ruwa A Shekarar 2024

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai 

November 17, 2025
Tsohon Firaministan Japan Ya Soki Kalaman Takaichi Dangane Da Batun Yankin Taiwan

Tsohon Firaministan Japan Ya Soki Kalaman Takaichi Dangane Da Batun Yankin Taiwan

November 17, 2025
Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC

Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC

November 17, 2025
Hakimi, Osimhen Da Salah Ƴan Wasan Da Ke Takara A Ƙyautar Gwarzon Afrika

Hakimi, Osimhen Da Salah Ƴan Wasan Da Ke Takara A Ƙyautar Gwarzon Afrika

November 17, 2025
Tsohuwar Firaministan Bangaladesh Sheikha Hasina,

An Yanke Wa Tsohuwar Shugabar Bangladesh Hukuncin Kisa

November 17, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi

Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi

November 17, 2025
Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka

Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka

November 17, 2025
Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda

Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda

November 17, 2025
Sarki Sanusi Ya Shawarci Unguwannin Da Suka Fuskanci Matsalar Tsaro Su Sa Idon

Sarki Sanusi Ya Shawarci Unguwannin Da Suka Fuskanci Matsalar Tsaro Su Sa Idon

November 17, 2025
Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

November 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.