Kashi 71 cikin 100 na mutanen Nijeriya ba su aminta da bangaren shari’ar kasar ba, in ji wani sabon rahoto.
Rahoton mai suna ‘The State of Freedom in Nigeria Report’, wanda kungiyar Anvarie Tech and ResearcherNG da Bincika Insights suka fitar tare da taimakon wata kungiya mai suna National Endowment for Democracy da ke Washington DC, Kasar Amurka.
Da take gabatar da rahoton, Farida Adamu, babbar shugabar shirin, Anvarie Tech, ta ce ta tantance ra’ayoyin ‘yan kasa kan ‘yancin fadin albarkacin baki, shiga siyasa, bin doka da kuma cin hanci da rashawa daga ranar 15 ga Nuwamba zuwa 10 ga Disamba, 2021.
Ta ce, ta tattauna da mutane 1,861 a yankuna shida na bangaren siyasa a kasar Nijeriya.
Rahoton ya ce kashi 71 cikin 100 na ‘yan Nijeriya ba su aminta da bangaren shari’a ba, kashi 65.2 cikin 100 kuma ba su aminta da hukumomin gwamnati da aka kafa domin yaki da cin hanci da rashawa ba, sannan kashi 40 cikin 100 ba su yarda ana zabe na gaskiya da adalci ba a Kasar.