Rahoton da hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar a yau Laraba, ya nuna cewa, jimilar darajar kayayyakin da ake shige da fice da su a kasar Sin cikin watanni shida na farkon bana, ya kai yuan triliyan 19.8, kwatankwacin dala tiliyan 2.94.
Idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, an samu karin kaso 9.4, kana rubu’i na 8 ke nan a jere da bangaren ke samun tagomashi. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)