Sama da mutum 500 ne suka ci gajiyar tallafin dogaro da kai a Jihar Jigawa. Gidauniyar Qatar da Gidauniyar Malam Inuwa wacce shugaban (NITDA) Kashifu Inuwa ya kafa su ne su ka ba da tallafin.
Gabatar da tallafin ya gudana a ranar Litinin a hedikwatar gidauniyar da ke HaÉ—ejia, Jigawa.
Shugaban gidauniyar Dr. Hussaini Baban ya bayyana cewa mata 200 an tallafa musu da kekunan É—inki an kuma tallafawa wasu mutum 300 da injin malkaÉ—e sai kuma mutum 3 an ba su Kwamfiyuta da mutum 13 da aka ba wa kayan aikin kafinta, sai wasu 13 da aka ba wa Baburan hawa na guragu.
Gwamnan Jigawa wanda mataimakinsa Umar Namadi ya wakilta tare da sarkin na Haɗejia Alhaji Adamu Maje sun godewa shugaban na NITDA da gidauniyar tasa da ta ƙasar ta Qatar.
Sauran manyan baƙi a wurin taron sun haɗa da shugabannin ƙananan hukumomi da ƴan majalissu, inda daga ƙarshe kuma su ka ziyarci wuraren da za su sake aiwatar da ginin gidaje da makarantu bayan sun buɗe wanda su ka yi.
Kashifu Na ÆŠaya Daga Cikin Wanda Talakawan Nijeriya Ke Amfana Da Dukiyarsa
Kashifu Inuwa na É—aya daga cikin mutane da dama da ke yin tasiri a É“angarensa, wanda bai ci ya cinye bai tuna da na Æ™asa da shi ba ko da bai sawa cikinsa komai ba. A Nijeriya yana É—aya daga cikin mai ba da agaji ga jama’a ta kowanne É“angare na wanda zai iya aiwatarwa.
Kashifu shi ne wanda ke ba da gudummawar kuÉ—insu, lokaci, tare da gogewarsa da gwaninta ko basira don taimakawa wasu da samar da mafi kyawun duniyarsu ta nuni da azasu hanya mai kyau, yana mai da hankali da mayar da hankali ga al’umma, yin canji da samar da canji mai kyau.
Duk wannan aikin agajin da ya ke yi ba shi da alaƙa da siyasa ko naɗin gwamnati, ga jama’ar da masu hannu da shuni ke ganawa da ƙungiyoyin ƙasa-da-ƙasa, domin kare al’ummarsa ‘yan Nijeriya baki ɗaya.
“Rayuwar sadaukarwa irin ta Kashifu abin sha’awa ce ga kowa daga cikin mu, sirrin rayuwa shi ne bayarwa, lokacin da kuke badawa, domin kaima idan kaba wani Allah zai ninka maka, don haka muna roÆ™on yaci gaba da badawa kar ya daina”, kamar yadda Tony ya bayyana.
Muna roƙon Allah ya ƙara maka Malam Kashifu matsayi mafi ɗaukaka, sannan ya maka kyakkywan ƙarshe, tare da gina maka gida a Aljannah.