Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ya dawo Abuja a yau Lahadi bayan wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 79 (UNGA) da aka gudanar a New York.
A cewar mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha, Mataimakin Shugaban ƙasa ya gabatar da jawabin ƙasa na Nijeriya yayin muhawarar bai ɗaya tare da halartar wasu tarurruka na ƙasa da ƙasa da kuma abubuwan da suka gudana a gefe.
- Manyan Batutuwan Taron Sanatoci Kan Gyaran Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya A Kano
- Gwamnan Kano Ya Nada Hauwa Isah Ibrahim Manajan Daraktan ARTV
Bayan dawowarsa, Mataimakin Shugaban ƙasar zai kasance tare da Shugaba Tinubu wajen halartar abubuwan da aka shirya don tunawa da cikar Nijeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai.