Gamnatin tarayyar Nijeriya ta buƙaci masu sayar da kayayyakin abinci da su rage farashi ta yadda masu amfani da kayan abincin za su samu saui a daidai lokacin da hauhawar farashin kayayyaki ya ragu a watan Janairu zuwa kashi 24.48.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa Ministan Noma da Albarkatun kasa, Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a ranar Talata a yayin bikin ranar gonakin alkama na shekarar 2025 a kauyen Dabi da ke karamar hukumar Ringim a Jihar Jigawa.
- Hanyoyi Biyar Da Gwamnatin Tarayya Ta Samar Don Dakile Karancin Abinci A 2025
- Gwamnatin Kebbi Ta Samar Da Tirela 300 Na Abinci Don Rabo Da Azumi
Ya yi tir da halin rashin mutunci da wasu ‘yan kasuwa ke nunawa wajen kin nuna rage farashin kayayyaki, yana mai bayyana hakan a matsayin rashin kishin kasa kuma ba za a amince da shi ba.
“Gwamnatin tarayya tana sane da yadda aka samu raguwar farashin kayan abinci a manyan kasuwanni, musamman na kayan masarufi kamar su gari, sukari, shinkafa, da taliya.
“Sai dai kuma yawancin dillalai da masu yin burodi, da masu shagunan sun ki yin la’akari da wannan ragi na farashin siyar da kayayyakinsu, wanda hakan ya hana ‘yan Nijeriya samun saukin da ya kamata.
“A watannin da suka gabata, masu ruwa da tsaki a cikin dillalan sun nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyakin abinci. Yanzu da farashin ya ragu, kamar garin da ya fadi daga naira 81,000 a kowace buhu zuwa kasa da naira 60,000, da taliya wanda ya fadi daga naira 20,000 zuwa naira 15,000.
“Adalci ne a bar masu amfani da kayayaki su amfana da wannan rage farashin abincin da aka samu,” in ji Kyari.
An dai bayar da rahoton cewa, hauhawar farashin kayan abinci ya ragu zuwa kashi 24.48 da kuma kashi 26.08 a watan Janairun 2025, inda ya ragu daga kashi 34.8 bisa dari da kuma kashi 39.84 a watan da ya gabata, sakamakon sake fasalin farashin kayan masarufi a kasar.
A halin da ake ciki, Cibiyar Inganta Kamfanoni masu zaman kansu ta bayyana cewa raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya a watan Janairun 2025 ba ya kai ga rage farashin kayayyaki da ayyuka.