Masu karatu assalamu alaikum wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh. Barkan mu da sake saduwa a filinmu na Dausayin Musulunci. A wannan mako za mu tabo abubuwan da suka shafi kayan tarihi da Manzon Allah (SAW) ya yi amfani da su tun daga na gida zuwa na yaki. Sai dai za mu karasa darasin da muke yi a kan kyawawan halayen Annabawa da ke nuni da cikarsu, Alaihimus Salam.
Kamar yadda muka yi bayani a karashen darasin na makon jiya, watakila an ce da Annabi Isah Dan Maryam sabida yawan tafiya a kasa, “da ka riki Jaki” sai ya ce, ina da girma a wurin Allah da har sai ya shagalantar da ni da Jaki. Annabi Isah ya kasance yana daura buzu ajikinsa, yana cin tsirrai, irin su kulubutu da irya da dai sauransu, bai kuma taba mallakar gida ba, duk inda barci ya riske shi a nan zai kwanta, ya fi son a kira shi da ‘Talaka’.
Wata kila an ce, Annabi Musa yayin da ya isa kasar Madyana(Falasdinu), ya kasance ana iya ganin korayen ganye na tsirrai da yake ci a cikinsa sabida hasken rana.
Annabi (SAW) ya ce, Annabawan da suka zo kafin ni, sun kasance ana jarrabar dayansu da talauci da kwarkwata, sai wannan ya zama mafi soyuwa a wurin Annabawan da a basu dukiya.
Annabi Isah ya ce wa wani Alade da ya hadu da shi a kan hanya, “kama hanyarka in kama tawa ba tsangwama”, kila sai aka ce masa, ‘Alade ne fa!’, sai ya ce, ina tsoron kar harshena ya saba da fadin mummunar magana.
Annabi (SAW) ya ce, “Abincin Annabi Yahya, ya kasance ganye ne”. Akwai addinatai da haramun ne su ci abu me rai, kamar Buda amma Musulunci ya halatta a yanka abu mai rai na daga dabbobin da Shari’ar Musulunci ta halatta kamar Rakumi, Saniya, Rago, Dan Akuya, Tsintsaye da makamantansu.
Annabi Yahya ya kasance kusan ko da yaushe yana kuka sabida tsoron Allah, har ana iya ganin shaidar hawaye a fuskarsa, ya kasance yana cin abinci tare da namun daji don karya ya cakudu da mutane su yi gulma. Wata rana Annabi Yahya ya hadu da Annabi Isah yana dariya, sai ya ce masa “kana dariya kamar ka amince wa Azabar Allah, sai Annabi Isa ya ce masa, kai kuma irin wannan tsanani kamar ka yanke wa Rahamar Ubangiji.”
Imam Dabri ya ruwaito Hadisi cewa, Annabi Musa ya kasance yana yin rumfa da ganyen bishiyoyi, kwanon cin abincinsa dutse ne aka fafake, in zai sha ruwa, baki yake tsomawa a ciki kamar yadda dabbobi ke shan ruwa don kankan da kai ga Ubangijinsa da abin da ya girmama shi da shi (yana magana da Ubangiji).
Annabi Yakubu yayin da dansa Annabi Yusuf ya dauko shi zuwa Misra bayan ya zama Sarki, sai ya umurci danshi da a yi masa rumfa da irin ganyen bulubutu irin yadda ya saba a Madyana, ga manyan gine-gine a gidan sarki amma da an shigo bangaren Annabi Yakub, sai ka ga kamar daji sabida kankan da kai ga Allah.
Labarun Annabawa cikin irin halayensu, duka suna nan a rubuce. Siffofin Annabawa cikin cika (Kamala) da kyakkyawan dabi’u da kyakkyawar cika, sanannu ne ba sai an tsawaita ba cikin bayaninsu.
Wannan Babin Zai Yi Magana A Kan Kayan Tarihi Da Kuma Zuhudun Annabi (SAW)
Yana daga cikin kayan yakin Annabi (SAW), yana da Takubba guda 9, wanda yanzu haka, suke gidan Tarihi da ke Kasar Turkiyya.
Sunan Takubban Annabi (SAW), su ne:
1.Zul Fikari – Annabi (SAW) ya bayar da ita ga Sayyadina Ali
2.Alma’asuru – Takobin mahaifinsa, Abdullahi. Akwai suna akanta, Abdullahi bin Abdulmudallib
3.Alkadid
4.Al’addu
5.Kula’i
6.Alhatfu
7.Albattar
8.Arrasubu
9.Almikzamu
Takobi Kula’i da Alhatfu da Albattar duk kirar Annabi Dawud ne, Annabi ya samu ganimarsu a yakin banu Kainuka’a.
Albattar, ita ce takobin Annabawa, sabida kusan Annabawa Bakwai ne suka mallake ta kuma suka rubuta sunansu a jikinta. Na Daya Annabi Dawud; na Biyu, dansa Annabi Sulaiman; na Uku, Annabi Musa; Na Hudu, Annabi Haruna; na Biyar, Annabi Yasa’u; na Shida, Annabi Isah sai na Bakwai, Annabi Muhammad (SAW).
Alhatfu, itama kirar Annabi Dawudu ce, ana cewa, ba karamin Sadauki ne zai iya daukarta farad-daya ba.
Yana daga cikin al’adar Larabawa, komai sai sun ambata masa suna har kofin shan ruwa ko dabbobi. Yana daga cikin al’adarsu, sanya wa ‘ya’yansu sunaye marasa kyau amma bayinsu su ambace su da suna mai kyau. Kila an ce musu, me yasa hakan? Sai suka ce, bayinmu namu ne, amma ‘ya’yanmu mun tanade su ne sabida makiyanmu, shi ya sa muka sanya musu sunaye masu kaushi (Kulaibu, Haidaru, …).
Sunan Sulke (rigar yaki) na Annabi (SAW), akwai:
1.Zatil Huduri
2.Zatil Hawashi
3.Fiddatu
4.Sugdiyyatu
5.Bakra’u
6.Karmuku
7.Zatil Wushahi
Sugdiyyatu da Fiddatu suna daga cikin Kirar Annabi Dawudu wanda Annabi ya gada a wurin Banu Kainuka’a.
Sunan Bakan harbi na Annabi (SAW), akwai:
1.Takra’u
2.Katumu
3.Sharhatu
4.Zaura’u
5.Rauha’u
6.Asfadadu
Garkuwar Annabi (SAW), akwai:
1.Zaluku
2.Kutaku
3.Mai mu’ujiza, Annabi ya gaje ta a wurin Yahudawa amma tana dauke da hoton dabba a jiki sai Annabi (SAW) ya dora hannu a kan hoton, nan take ya shafe hoton.
Masun Annabi (SAW), akwai:
1.Musmi
2.Masmawi
3.Musnawi, akwai guda biyu wanda Annabi (SAW) bai musu suna ba.
Musmi da Masmawi, ana zaton duk na Annabi Dawuda ne da Annabi ya gada a wurin Yahudawan Banu Kainuka’a.
Sunan Kwagiri (Sanda mai lankwashasshen kai amma karshenta Mashi ne) na Annabi (SAW), akwai:
1.Harbatu
2.Harbatun Sagiratu
Sunan gidan kibiyoyi na Annabi (SAW), akwai guda daya, ana kiransa da Kafuru.
Sunan Belt (igiyar damara ta kayan yaki) na Annabi (SAW), yana da kofofi na Azurfa guda Uku da ake zura igiya a ciki, gefensa an sa masa Azurfa amma Annabi (SAW) bai masa suna ba.
Annabi (SAW) yana da Kwalkwali (Hular Karfe) guda biyu, su ne: Sugugu da Muwasshaha.
Annabi (SAW) yana da ‘Tempol’ (Dakin da ake yi yayin tafiya ko yaki), sannan kuma yana da Sanduna guda Uku: Urjum, Kanjiri da Almamshuku. Akwai kofunan shan ruwa guda bakwai: Rayyanu, Mugisa, Kadhu, Tauru, Mikbaru, akwai na Tangaran da na Azurfa amma ba a ambace su da wani suna ba.
Annabi (SAW) yana da babban kwano na cin abinci mai suna Algarra’u da abin wanka (kamar kwarya amma ta tagulla), yana da abin shafa Mai wanda aka yi da Hauren Giwa. Annabi (SAW) yana da Jaka ta ratayawa akwai madubi a cikinta da ‘Comb’ na taje gashi da aka yi shi da Hauren Giwa, akwai Tandun kwalli a cikinta da Asiwaki.
Annabi (SAW) yana da kwanon Awo, yana da Katifa da Gado, yana da Zobe guda biyu, akwai na Bakin Karfe da aka lallauya masa Azurfa da kuma na Azurfa – An rubuta Muhamadu Rasulullah a kan Azurfar, an ruwaito cewa, Annabi (SAW) yana amfani da zoben wurin buga ‘stamp’ dinsa in an yi rubutu.
Annabi (SAW) yana da Alkebba guda Uku, Sundusu Koriya, Jubba mai kokuwa sai Abaya mara kokuwa, akwai rawani na Annabi (SAW) guda biyu, akwai Sahabu (Girgije) da kuma Aswad (Baki wanda aka yi Fat’hu Makkata da shi), Annabi (SAW) yana da Tutar Kasa (Mai Launin Fari) da Tutar yaki mai suna Gaggafa, mai launin Baki.
Annabi (SAW) yana da Mayafi wanda ake ratayawa bayan an sa kaya.