Kungiyar ’yan jarida masu bibbiyar harkokin wasanni ta duniya wato AIPS, ta fitar da kayayyakin aikin jarida mafiya burgewa a shekarar 2022, da ’yan jaridar suka zaba ta hanyar jefa kuri’a, kuma gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta kai matsayi na farko a wannan fage.
A yayin zabe na wannan karo, sassan uku na farko a samu kuri’un, su ne gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, da “cikakkiyar” gasar wasanni ta cin kofin Turai da aka yi a birnin Munich, wadda ta kunshi wasanni tara, da suka hada da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, da wasannin motsa jiki, da tseren kekuna, da wasan kwallon tebur da sauransu. Ta ukun kuwa ita ce gasar wasannin kasashe renon Ingila ko “Commonwealth” wadda ta gudana a birnin Birmingham.
AIPS ta bayyana a kan shafinta na yanar gizo cewa, a shekarar 2022, yawancin kayayyakin aikin jarida da aka yi amfani da su a wasannin suna da kayatarwa sosai, kuma gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, da aka gudanar a farkon shekarar 2022, ita ce mafi burgewa a cikinsu, sabo da an gudanar da wannan cibiyar watsa labarai ta gasar kamar yadda ’yan jaridu suke fata, har ma ta ba da hidima mai gamsarwa. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp