Kere-keren fahasa ne kawai za su kai matakin jan ragamar tattalin arzikin Nijeriya tare da kayan da take samarwa da sayarwa wajen ganin an dafa wa ci gaban da ake bukata, a cewar manajan gudanarwa na kamfanin Ink. Nigeria, Mista Ifeanyi Akosionu.
Akosionu ya shaida hakan bayan da kamfaninsa ya karbi lambar yabo a yayin taron ‘Africa Beacom of ITC Meria and Leadership awards’ (ABoLCT), wanda ya gudana a Legas a cikin makon nan.
Kamfanin ya lashe kambon mafi kwazo a bangaren fahasar sadarwar zamani da kuma kasancewa sa mai kwazo a bangare fasaha ta shekara.
- Manoma Za Su Amfana Da Tallafin Dala 25, 000 A Nasarawa
- Sanata Yari Ya Samar Da Taki Ga Manoman Zamfara A Kan Naira 20,000
Ya ce, “Lokaci ya yi da ya kamata Nijeriya da ‘yan kasarta su canja daga hanyoyin da suke bi na al’ada a bangaren fasaha su rungumi kere-keren fasahar zamani, wanda shi ne kawai zai jagoranci ragamar tattalin arziki a ga tasirinsa nan take a Nijeriya ta hanyar kayayyakin da ake hadawa da sayarwa domin taimaka wa ci gaban tattalin arziki,” ya shaida.
Ya ce kamfanin nasu ya sauya daga hanyoyin da yake bi na al’ada zuwa ga rungumar kere-kere wanda har hakan ya kaisa ga samun lambobin yabo a kai a kai na tsawon shekaru.
Da yake amsar lambar yabon a madadin kamfanin, Akosionu ya ce, “Ina farin cikin amsar wadannan lambobin yabon daga ABoICT. Tabbas lambobin yabon sun kara nuna mana irin aiki tukuru da jajircewa da dukkanin ma’aikatan kamfanin Ink. Nigeria ke yi.”
Mawallafi kuma babban editan ‘Nigeria Communications Week’, Mista Ken Nwogbo, ya ce, “Taron mika lambobin yabo da jerin laccocin an shirya su ne domin baje wa duniya kolin hazikan da Nijeriya ke da su a bangaren fasahar sadarwar zamani da kuma nuna karamci ga kungiyoyin da suka yi zarra wajen ba da gudunmawa ga ci gaban bangaren fasahar sadarwar zamani a Nijeriya.”