• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kin Biyan Bashi Daga Wasu Manoma Zai Kawo Cikas Ga Noman Shinkafa A Bana – Ɗan Madamin Samaru 

by Isa Gidan Bakko Zariya
4 months ago
Manoma

Mataimakin shugaban kungiyar masu noman shinkafa a Jihar Kaduna, Alhaji Hassan Tahir Tanimu (Dan Madamin Samaru), ya ce matsalar kin cika alkawarin biyan bashin da aka yi wa manoma shinkafa a Nijeriya zai iya kawo cikas ga noman shinkafa a wannan damuna da aka shiga. 

Alhaji Hassan wanda kuma shi ne shugaban kwamitin karbo bashin da aka yi wa manoman shinkafa daga shekara 2015 zuwa 2025, ya ce gwamnatin tarayya da kuma kamfanonin da suka hadu suka raba bashin sun dauki matakan ba-sani-ba-sabo ga dukkanin wanda aka ba shi bashin amma bai biya ba kamar yadda aka yi alkawari.

Ya ce majalisar tarayya ta yunkura kan batun noman shinkafa da aka ba manoma, kuma nan ba da jima wa ba za a fara daukar matakan da suka dace ga wadanda suka karbi bashin amma ba su biya ba.

A game da matsalolin tsaro da suka addabi wasu kananan hukumomi da suka hada da Giwa da Birnin Gwari da Chukun da kuma Kachiya a Jihar Kaduna, ya ce a damunan bana batun noman shinkafa a wadannan kananan hukumomi ya kankama, babu kama hannun yaro.

Dan Madamin Samaru ya ce hakan ya faru ne a dalilin kokarin da gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya yi na matakan samar da tsaro a wadannan kananan hukumomi.

LABARAI MASU NASABA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

Alhaji Hassan ya ce duk da matsalolin tsaro da aka samu a kananan hukumomin, Jihar Kaduna ce kan gaba a noman shinkafa a daukacin jihohin da suke Nijeriya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

October 3, 2025
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

October 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Next Post
Ba Tsoro Ne Yasa Muka Amince Da Sulhu Da Ƴan Bindiga Ba – Gwamnatin Sokoto

Ba Tsoro Ne Yasa Muka Amince Da Sulhu Da Ƴan Bindiga Ba – Gwamnatin Sokoto

LABARAI MASU NASABA

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.