Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya umarci gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON) da ya maida hankali wajen yaɗa kyawawan labarai da shirye-shirye game da irin gudunmawar da Nijeriya ke bayarwa ga cigaban duniya.
Mataimakin Daraktan yaɗa labarai a ma’aikatar, Malam Suleiman Haruna, ya ruwaito a cikin sanarwa ga manema labarai da ya bayar cewa ministan ya yi wannan umurnin ne a lokacin da hukumar gudanarwa ta gidan rediyon ta kai masa ziyarar aiki a ofishin sa a Abuja a ranar Talata, 19 ga Disamba, 2023.
Ministan ya yi kira ga VON da ta isar da saƙon damarmakin da ke akwai, da haɗin gwiwa, da ingantuwar ƙasar Nijeriya ta yadda Nijeriya za ta ci moriyar Zuba Jari Kai-tsaye daga Waje.
Ya ce idan an samar da kyakkyawan yanayin yin kasuwanci, to gwamnati za ta samun ƙarin ayyukan yi da kuma kuɗin shiga.
Ya ce: “Ku na da rawar da za ku taka wajen aikin sauya fasalin zamantakewa da gwamnatin Tinubu ta sanya a gaba a yanzu.
“Tilas ne ku riƙa isar da saƙon mu na ƙaruwar arziki da damarmakin da ke akwai, tare da jama’a ƙwararru a fannoni daban-daban don a jawo ra’ayin masu zuba jari da kuma masu yawon shaƙatawa zuwa Nijeriya.
“Nijeriya ta na kan hanyar ta ta samun martaba; tilas mu ƙarfafa gwiwar masu harkokin kasuwanci su shigo ciki a dama da su domin su amfana.”
Ministan ya ce ya na sane sosai da cewa sassa da dama na Nijeriya su na buƙatar a tallafa masu domin su shigo cikin wannan tsarin na sauya fasalin zamantakewa. Ya ce duk da hakan, gwamnatin ta na yin bakin ƙoƙarin ta domin magance matsaloli.
Akwai buƙatar gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON) ya isar da wannan saƙon ga duniya, inji shi.
Tun da farko a nasa jawabin, sai da Darakta-Janar na Muryar Nijeriya, Alhaji Jibrin Baba Ndace, ya bayyana cewa hukumar gudanarwa da ma’aikatan gidan rediyon sun kawo ziyarar ne domin su sanar da ministan irin tsarin aiki da su ka fito da shi kuma su shaida masa cewa su na bin dukkan tsare-tsaren gwamnatin Tinubu sosai da sosai.
Darakta-Janar ɗin ya ba ministan tabbacin cewa duk da yake su na watsa shirye-shirye cikin harsunan ƙasashen waje guda huɗu ne, yanzu su na da burin su faɗaɗa zuwa harsunan wasu manyan ƙasashen irin su Chaina da Indiya, waɗanda su na gudanar da harkokin kasuwanci a Nijeriya.