• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kiristoci Kada Su Damu Da Takarar Musulmi 2 – Shugaban Jam’iyyar APC

by Sadiq
3 years ago
APC

Shugaban jam’iyyar APC, mai mulkin Nijeriya, Sanata Abdullahi Adamu, ya shawarci mabiya addinin Kirista da su daina wata fargaba a kan tsayar da dantakarar shugaban kasa na 2023, Musulmi da mataimakinsa Musulmi da jam’iyyar ta yi.

Shugaban ya ce yanayin halin da siyasar kasar ke ciki ne a yanzu ya janyo hakan, wanda idan har jam’iyyar na son ta ci zaben 2023 sai ta yi hakan, amma ba abu ne da wani zai so ba a ce an yi wannan tsari.

  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Umarnin Sayar Da Takin Noma Miliyan 1.7 Ga Manoman Jihar
  • Ya Kamata Buhari Ya Gaggauta Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU – Femi Falana

Sanata Adamu ya ce zaben Kashim Shettima a matsayin mataimakin Bola Ahmed Tinubu, abu ne yin Allah.

Da yake yi wa manema labarai bayani bayan wata ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari, a Daura, Jihar Katsina a jiya Laraba, tsohon gwamnan na Nasarawa, ya ce bai kamata wannan zabi ya zama abin korafi ba ga mabiya addinin Kirista.

“Gaskiyar lamari shi ne, ba abin da Allah yake yi haka kawai. Allah yana da dalilinsa na samar da manyan addinai biyu a kasar nan, kuma kowane daga cikinsu, yana da mutanen da suke da dalilin binsa kuma suna da hakki suma.”

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

”Akwai lokacin da Kirista ya jagoranci kasar nan. Yanzu kuma lokaci ne da Musulmi ke shugabantar kasar, ba za mu musanta wanna ba. Ba za mu iya samun lalle abin da muke so ba a wani lokaci, a ce dukkanin mu, mun amince da abu daya,” in ji shi.

Ya kuma kara da bayanin cewa, ” Ba lalle ba ne sai dukkaninmu mun kasance Musulmi ba ko kiristoci. Nufi ne na Allah a wannan lokacin cewa Shettima zai kasance mataimakin shugaban wannan babbar kasa, idan muka ci zabe. Abin da muke fata da kuma addu’a, wanda kuma muna kokarin cin zaben.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu
Siyasa

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

October 20, 2025
Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027
Siyasa

Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

October 17, 2025
Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu
Siyasa

Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

October 16, 2025
Next Post
Dangantaka Tsakanin Nijeriya da Sin Ta Kara Karfi Yayin Da Jirgi Ya Fara Tashi Zuwa Guangzhou

Dangantaka Tsakanin Nijeriya da Sin Ta Kara Karfi Yayin Da Jirgi Ya Fara Tashi Zuwa Guangzhou

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

October 20, 2025
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

October 20, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

October 20, 2025
Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

October 20, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

October 20, 2025
An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.