A daidai lokacin da ka samu wasu ‘yan tsagera a yankin Kudancin kasarnnan suka kashe wata mata mai suna Harira ‘yar asalin Jihar Adamawa tare da yaranta hudu, wani tsohon Sanata a Jihar Adamawa kuma Shugaban kungiyar Matasa na yankin Arewa maso gabas, masu neman cigaba da zaman lafiya, Alhaji Abdulraham Buba Kwachma ya yi tir da kisan da aka yi wa Hariran ya ce, lamarin ya kasance na bakin ciki da tashin hankali, wanda duk wani mai imani da tsoron Allah ba zai so yaga irin wannan abin bakin cikin ba a tarihin rayuwarsa.
‘’Muna nema musu gafarar Allah, ya kuma jikansu, muna addu’ar Allah ya ba mijinta hakuri tare da dukkan al’umma yankin Adamawa da Nijeriya baki daya, abu ne da bamu ji dadinsa ba, ya kuma kamata a gaggauta daukar matakin dakike faruwar hakan” in ji shi.
Alhaji Abudurahaman Buba Kwacahm ya kuma bukaci gwamnati ta gaggauata daukar matakin kare al’umma Arewacin kasar nan da ke zaune a yankin kudanci Nijeriya, “Bai yiwu mu zura ido muna gani ana kashe mana al’umma ba ba tare da wani dalili ba a yankin kudancin kasar ba kuma tare da an dauki matakin kariya ba, in har al’ummamu suka dauki mataki lallai abin ba zai yi kyau ba” in ji shi.
Ya kuma yi nuni da cewa, halin da al’ummar arewa ke ciki ya ishesu, ‘‘Muna fama da masu garkuwa da mutane ga ‘yan ta’adda, an hanamu noma a kullum ana kashe mutane amma kuma sai gashi wadanda suke je neman abincinsu a yankin Kudu ana kashe su babu kakkautawa, wannan ba zamu lamunta ba” in ji shi.
Ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da dukkan rundunonin tsaro su tabbatar da kare al’mmau Nijeriya a duk inda suke don a tabbatar da zaman lafiya tare da kuma nema wa wadanda aka kashe hakkinsu, muna kuma bukatar a hukunta duk wadanda suke da hannu a wadannan lamarin kamar yadda doka ta tanada.
Daga karshe ya nemi al’umma su zauna lafiya tare da bin doka a dukkan inda suka samu kansu.