Hajiya Maryam Umar Kofar Mata, Shugabar Gidauniyar Maryam Kofar Mata, Guda cikin fulogan tafiyar Gidan A A Zaura, sannan ‘yar gaba dai gaba dai a tafiyar Dakta Nasiru Yusif Gawuna.
Mace ta farko data Jagoranci rabawa Mata da Maza tallafi domin Dogaro dakai. A tattaunawartar ta Wakilinmu na Kano Abdullahi Muhammad Sheka.
- Nnamdi Kanu Ya Maka Gwamnatin Tarayya A Kotun KoliÂ
- Gwamnatin Kaduna Ta Jajanta Wa Iyalan Mutane 15 Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe
Maryam Kofar Mata ta bayyana dalilin samar da gidauniyar tallafa wa Mata, Marayu da masu karamin karfi, haka kuma ta bayyana matsayar matan Jihar Kano a zaben shekara ta 2023. Ga dai yadda tattaunawar ta Kasance:
Za muso ki gabatar wa da mai karatu kanki da kanki?
Alhamdulillahi kamar yadda aka sani ni sunana Hajiya Maryam Kofar Mata Shugabar Gidauniyar Maryam Kofar Mata ‘Yar Takarar Majalisar Wakilai a Karamar Hukumar Birni da kewaye a baya, guda cikin ‘yan gaba dai Gaba dai na Gidan AA Zaura, sannan guda cikin jagorori Mata Masu yayata kyawawan manufofin Dakta Nasiru Yusif Gawuna dan Takarar Gwamna a Jam’iyyar APC a zaben Shekara ta 2023.
Mene ne dalilin kafa wannan Gidauniya taki?
Kamar yadda aka sani Mata sunfi kowa sanin matsalar Marayu da Mata kasancewarsu masu karamin karfi, wannan dalili yasa na yanke shawarar kafa wannan gidauniya, wadda zuwa yanzu Mata da matasa sama da 300 ne suka amfana da ayyukan da take. Kuma alhamdulillahi akwai rukunin Jama’a daban-daban da suka hada da Mata, Zawarawa, Marayu da marasa galihu da wannan Gidauniya ta duba ta fuskar da za tu kai masu dauki.
Baya ga ayyukan Gidauniyar, an sanki cikin gogaggun ‘yan siyasa Mata da ake damawa dasu, shin ko mene mahangar ki kan zaben shekara ta 2023
Alhamdulillahi yanzu da aka fara kada gangar zaben Shekara ta 2023, daka cikin masu neman kujerar Gwamnan Kano babu wanda ya fi da cewa kamar Dakta Nasiru Yusif Gawuna da sauran ‘yan takarkarun mu daga sama har kasa na Jam’iyyar APC, wannan tasa muka ga ba wanda yafi da cewa da jagorantar Jihar Kano kamar Gawuna da Garo. Haka kuma a Kano ta tsakiya jama’a sun gamsu da nagartar AA Zaura.
Ana ganin kamar ana barin Mata cikin wasu al’amuran siyasa, shin ko me zaki ce a kan haka?
Idan ma ana samun irin wannan wariyar sai dai a wasu jihohin, amma banda Jihar Kano, musamman karkashin Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, domin mu a Jihar Kano ba abinda za muce da Khadimul Islam sai godiya, domin a yanzu ba sai gobe ba, babu wata jiha a tarayyar Nijeriya da takai Jihar Kano baiwa Mata mukamai masu Gwabi Gwabi kamar Kano, dubi Kwamishinoni har guda biyu, Shugabar Ma’aikata, ma’ajin Jam’iyyar APC ta Jihar Kano, manyan mashawarta na musamman da mataimaka da sauransu. Saboda haka mu a Jihar Kano lamarin sai godiya.
Kasancewarki mace, shinko wace rawa kike ganin zaku taka a kakar zaben shekara ta 2023?
Ina tabbatar maka da cewa Mata ne zasu fara yi wa ‘yan takarkarun mu na Jam’iyyar APC luguden kuri’u a lokacin zabe mai zuwa. Domin iyaye mata sun gamsu da kokarin Gwamna Ganduje da kuma mai dakinsa Farfesa Hafsat Ganduje wanda itace tare da jajircewar ta har aka kai ga samun nasarar shigar da mata dukkan mukaman da suke kai a halin yanzu, wannan kuma baya rasa nasaba da kyakkyawar tarbiyarta da kuma kishin cigaban Mata da Kananan yara a Jihar Kano.
Da me kike fatan a dinga tunawa dake?
“Kaunar tallafa wa Mata da Marayu tare da masu karamin karfi, musamman ma ganin haka na taso a gidanmu na ga mahaifana na hidimtawa Jama’a ba dare ba rana, wannan tasa na yi alkawarin ci gaba da wannan Hidima har zuwa karshen rayuwata.
Duk da cewar ke ba Makamar lissafin habe, da ace abaki damar auna Nasarorin Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Maki nawa zaki bashi?
Ai ko hasidin iza hasada yasan ta Ganduje ba irin tasu bace, shi ne Gwamna daya tilo da ya cika dakacin alkawuran da ya yi wa Jama’a harma da kari. Saboda Haka Khadimul Islam ya canci abashi maki dari bisa dari. Saboda haka muna tabbatarwa da Jam’iyyun Adawa su shafawa kansu Lafiya, domin Kano ta Gawuna da Garo ce da yardar Allah.
Mun gode kwarai da gaske
Nima na gode