• English
  • Business News
Friday, July 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kishin Mata Da Kananan Yara Ya Sa Na Kafa Gidauniyata -Maryam Umar

by Abdullahi Muh'd Sheka
3 years ago
in Manyan Labarai, Rahotonni
0
Kishin Mata Da Kananan Yara Ya Sa Na Kafa Gidauniyata -Maryam Umar
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Hajiya Maryam Umar Kofar Mata, Shugabar Gidauniyar Maryam Kofar Mata, Guda cikin fulogan tafiyar Gidan A A Zaura, sannan ‘yar gaba dai gaba dai a tafiyar Dakta Nasiru Yusif Gawuna.

Mace ta farko data Jagoranci rabawa Mata da Maza tallafi domin Dogaro dakai. A tattaunawartar ta Wakilinmu na Kano Abdullahi Muhammad Sheka.

  • Nnamdi Kanu Ya Maka Gwamnatin Tarayya A Kotun Koli 
  • Gwamnatin Kaduna Ta Jajanta Wa Iyalan Mutane 15 Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe

Maryam Kofar Mata ta bayyana dalilin samar da gidauniyar tallafa wa Mata, Marayu da masu karamin karfi, haka kuma ta bayyana matsayar matan Jihar Kano a zaben shekara ta 2023. Ga dai yadda tattaunawar ta Kasance:

Za muso ki gabatar wa da mai karatu kanki da kanki?

Alhamdulillahi kamar yadda aka sani ni sunana Hajiya Maryam Kofar Mata Shugabar Gidauniyar Maryam Kofar Mata ‘Yar Takarar Majalisar Wakilai a Karamar Hukumar Birni da kewaye a baya, guda cikin ‘yan gaba dai Gaba dai na Gidan AA Zaura, sannan guda cikin jagorori Mata Masu yayata kyawawan manufofin Dakta Nasiru Yusif Gawuna dan Takarar Gwamna a Jam’iyyar APC a zaben Shekara ta 2023.

Labarai Masu Nasaba

Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe

Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Okpebholo A Matsayin Zaɓaɓɓen Gwamnan Edo

Mene ne dalilin kafa wannan Gidauniya taki?

Kamar yadda aka sani Mata sunfi kowa sanin matsalar Marayu da Mata kasancewarsu masu karamin karfi, wannan dalili yasa na yanke shawarar kafa wannan gidauniya, wadda zuwa yanzu Mata da matasa sama da  300 ne suka amfana da ayyukan da take. Kuma alhamdulillahi akwai rukunin Jama’a daban-daban da suka hada da Mata, Zawarawa, Marayu da marasa galihu da wannan Gidauniya ta duba ta fuskar da za tu kai masu dauki.

Baya ga ayyukan Gidauniyar, an sanki cikin gogaggun ‘yan siyasa Mata da ake damawa dasu, shin ko mene mahangar ki kan zaben shekara ta 2023

Alhamdulillahi yanzu da aka fara kada gangar zaben Shekara ta 2023, daka cikin masu neman kujerar Gwamnan Kano babu wanda ya fi da cewa kamar Dakta Nasiru Yusif Gawuna da sauran ‘yan takarkarun mu daga sama har kasa na Jam’iyyar APC, wannan tasa muka ga ba wanda yafi da cewa da jagorantar Jihar Kano kamar Gawuna da Garo. Haka kuma a Kano ta tsakiya jama’a sun gamsu da nagartar AA Zaura.

Ana ganin kamar ana barin Mata cikin wasu al’amuran siyasa, shin ko me zaki ce a kan haka?

Idan ma ana samun irin wannan wariyar sai dai a wasu jihohin, amma banda Jihar Kano, musamman karkashin Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, domin mu a Jihar Kano ba abinda za muce da Khadimul Islam sai godiya, domin a yanzu ba sai gobe ba, babu wata jiha a tarayyar Nijeriya da takai Jihar Kano baiwa Mata mukamai masu Gwabi Gwabi kamar Kano, dubi Kwamishinoni har guda biyu, Shugabar Ma’aikata, ma’ajin Jam’iyyar APC ta Jihar Kano, manyan mashawarta na musamman da mataimaka da sauransu. Saboda haka mu a Jihar Kano lamarin sai godiya.

Kasancewarki mace, shinko wace rawa kike ganin  zaku taka a kakar zaben shekara ta 2023?

Ina tabbatar maka da cewa Mata ne zasu fara yi wa ‘yan takarkarun mu na Jam’iyyar APC luguden kuri’u a lokacin zabe mai zuwa. Domin iyaye mata sun gamsu da kokarin Gwamna Ganduje da kuma mai dakinsa Farfesa Hafsat Ganduje wanda itace tare da jajircewar ta har aka kai ga samun nasarar shigar da mata dukkan mukaman da suke kai a halin yanzu, wannan kuma baya rasa nasaba da kyakkyawar tarbiyarta da kuma kishin cigaban Mata da Kananan yara a Jihar Kano.

Da me kike fatan a dinga tunawa dake?

“Kaunar tallafa wa Mata da Marayu tare da masu karamin karfi, musamman ma ganin haka na taso  a gidanmu na ga mahaifana na hidimtawa Jama’a ba dare ba rana, wannan tasa na yi alkawarin ci gaba da wannan Hidima har zuwa karshen rayuwata.

Duk da cewar ke ba Makamar lissafin habe, da ace abaki damar auna Nasarorin Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Maki nawa zaki bashi?

Ai ko hasidin iza hasada yasan ta Ganduje ba irin tasu bace, shi ne Gwamna daya tilo da ya cika dakacin alkawuran da ya yi wa Jama’a harma da kari. Saboda Haka Khadimul Islam ya canci abashi maki dari bisa dari. Saboda haka muna tabbatarwa da Jam’iyyun Adawa su shafawa kansu Lafiya, domin Kano ta Gawuna da Garo ce da yardar Allah.

Mun gode kwarai da gaske

Nima na gode

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: GawunaGidauniyakanoKishiMata
ShareTweetSendShare
Previous Post

Sin Ta Kara Baiwa Zimbabwe Allurar Rigakafin COVID-19

Next Post

Abokai Na Zahiri Suna Zurfafa Huldar Zumunci A Sabon Zamani

Related

Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe
Manyan Labarai

Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe

3 hours ago
Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Okpebholo A Matsayin Zaɓaɓɓen Gwamnan Edo
Da ɗumi-ɗuminsa

Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Okpebholo A Matsayin Zaɓaɓɓen Gwamnan Edo

12 hours ago
Buhari Ba Mutum Ne Mai Son Abun Duniya Ba – Gowon
Manyan Labarai

Buhari Ba Mutum Ne Mai Son Abun Duniya Ba – Gowon

14 hours ago
Tinubu Bai Taɓa Ba Ni Umarnin Yin Ƙarya Ko Cin Zarafin ’Yan Jarida Ba – Minista
Manyan Labarai

Tinubu Bai Taɓa Ba Ni Umarnin Yin Ƙarya Ko Cin Zarafin ’Yan Jarida Ba – Minista

17 hours ago
Har Yanzu A Cikin PDP Nake, Ba Zan Koma APC Ko ADC Ba – Gwamnan Zamfara
Manyan Labarai

Har Yanzu A Cikin PDP Nake, Ba Zan Koma APC Ko ADC Ba – Gwamnan Zamfara

1 day ago
Sanata Natasha Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Ta Koma Majalisa Ba
Manyan Labarai

Sanata Natasha Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Ta Koma Majalisa Ba

2 days ago
Next Post
Abokai Na Zahiri Suna Zurfafa Huldar Zumunci A Sabon Zamani

Abokai Na Zahiri Suna Zurfafa Huldar Zumunci A Sabon Zamani

LABARAI MASU NASABA

Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Kai Matakin Kwata Fainal Bayan Doke Botswana

Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Kai Matakin Kwata Fainal Bayan Doke Botswana

July 10, 2025
Mataimakin Babban Magatakardan MDD: Sin Aminiya Ce Da Afirka Za Ta Iya Dogaro Da Ita

Mataimakin Babban Magatakardan MDD: Sin Aminiya Ce Da Afirka Za Ta Iya Dogaro Da Ita

July 10, 2025
Li Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da ALLi Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da AL

Li Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da ALLi Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da AL

July 10, 2025
Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe

Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe

July 10, 2025
Yadda JKS Ta Jure Tsawon Tarihin Gwagwarmaya Da Cimma Nasarori

Yadda JKS Ta Jure Tsawon Tarihin Gwagwarmaya Da Cimma Nasarori

July 10, 2025
An Kama Magungunan Jabu Na Fiye Da Naira Biliyan Ɗaya A Kano

An Kama Magungunan Jabu Na Fiye Da Naira Biliyan Ɗaya A Kano

July 10, 2025
Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adam

Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adam

July 10, 2025
Majalisar Ta Kwace Shugabacin Kwamitin Da Natasha Ke Jagoranta

Majalisar Ta Kwace Shugabacin Kwamitin Da Natasha Ke Jagoranta

July 10, 2025
An Bude Taron Ministoci Kan Wayewar Kai A Birnin Beijing

An Bude Taron Ministoci Kan Wayewar Kai A Birnin Beijing

July 10, 2025
Shiri Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Tabbatar Da Ci Gaban Kasar Sin

Shiri Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Tabbatar Da Ci Gaban Kasar Sin

July 10, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.