Fadar Shugaban Kasar Najeriya, ta yi wa Tsohon Shugaban Kasar Nijeriya, Goodluck Jonathan maraba da yunkurinsa na sake tsayawa takarar shugabancin kasa a zaben 2027.
A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce, ‘dan Nijeriya na sane da mulkin Jonathan din da ya yi a shekarun baya, sannan ba su manta da irin wahalhalun da suka sha ba.
- Gwamna Lawal Ya Gwangwaje Kamfanin Sufurin Mota Na Zamfara Da Motoci 50Â
- Dubban Matasan Kano Sun Yi Zanga-zangar Lumana Domin Goyon Bayan CP AI Bakori
Idan ba a manta ba, tsohon shugaban kasar ya mulki Nijeriya a daidai lokacin da kungiyar Boko Haram ke kan ganiyarta, musamman wajen kaddamar hare-hare iri daban-daban a kan wadanda ba su ji ba, ba su kuma gani ba.
Har ila yau, a baya-bayan nan dai an ta faman samun karuwar kiraye-kiraye a tsakanin wasu dan jam’iyyar hamayya ta PDP tare da matsin lamba kan Jonathan din ya sake fitowa takara a zabe mai zuwa (2027).
Sai dai, fadar shugaban kasar ta ce, ko kadan Jonathan ba tsaran takarar Tinubu ba ne, idan aka yi la’akari da yadda mulkinsa ya kasance a baya da kuma yadda a yanzu ta ce shugaba Tinubun na kokarin inganta kasar, musamman ta fuskar fannin tattalin arziki.
Wannan sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ya sanya wasu na ganin kamar tana fargabar fitowar takarar Jonathan din ne.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp