A daidai lokacin da wa’adin mulkin gwamnan Jihar Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje ke karewa, ya roki gafarar wadanda ya saba musu a yayin gudanar da mulkinsa na tsawon shekaru takwas a Jihar Kano.
Sai dai kuma a wani martani da ya mayar kan yafiyar Gwamna Ganduje mai barin gado, tsohon kwamishinan ayyuka da ababen more rayuwa, Muaz Magaji ya ce “Eh na yafe maka, amma ba zan taba mantawa da yadda kuka kulla makarkashiyar kawar da ni daga doron kasa ba a lokuta da dama.”
- Kwaliyyar Da Samari Da ‘Yanmata Suka Tsara Don Burgewa A Wannan Sallar
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Kwaso Daliban Nijeriya Bayan Barkewar Rikici A Sudan
Ana sa ran Gwamna Ganduje zai kammala wa’adinsa na biyu na shekaru takwas nan da watan gobe tare da mika ragamar mulkin Jihar Kano ga zababben gwamna, Abba Kabir Yusuf.
Da yake karin haske daga kalamansa, Ganduje ya ce “Na yafe wa duk wanda yayi min laifi ko ya wulakanta ni, domin haka, ina neman gafara ga duk wanda na yi wa ba daidai ba”.
A cewarsa, ya yi hakan ne bisa karantarwar addinin Musulunci, inda ya kara da cewa afuwa na da matukar muhimmanci a cikin koyarwar addinin Musulunci.
“Aikina na gwamnan Jihar Kano ya zo karshe, kuma wannan gaisuwa ce ta bankwana. Ina muku fatan alheri. Ga wadanda muka bata wa rai, ina rakonsu su gafarta mana, a nawa bangaren na yafe wa wadanda suka zalunce ni komai girman laifin. “
Bayan ya kammala jawabi, “Tsohon kwamishinan ayyuka da ababen more rayuwa na Ganduje, Mu’az Magaji, wanda ya halarci taron ya tashi ya ce, “Eh, na yafe maka, amma ba zan manta da yadda kuka kulla makircin kawar da ni daga doron kasa ba a lokuta da dama”.
Sai dai Magaji a cikin shafinsa na Facebook ya ambaci wurare uku da ya tsallake rijiya da baya da ake zargin tsohon ubangidansa ne ya shirya masa gadar zare.
Ra’ayoyin Kanawa Kan Neman Gafarar Gwamna Ganduje
Ganduje Bai Cika Sharadan Tuba Ba, Saboda Haka Ba Da Gaske Yake Yi Ba – Musa Falaki
Sheikh Musa Falaki yana daga cikin masu yawan kallon yadda abubuwan gwamnati ke tafiya ta fuskar shari’a. Kan bautun neman gafarar Ganduje, Falaki ya bayyana cewa Ganduje bai cika sharadan tuba ba, domin kuwa cikin sharadan tuba na farko ma shi ne, yin nadama kan abubuwan da suka wakana, saboda haka rashin wannan nadama ya sa Kanawa ke kallon wannan neman gafara a matsayin wasa da hankali, musamman kasancewar neman gafara abu biyu ne, ko dai neman gafara kan abin da ka aikata wa Allah tsakaninka da shi, sannan akwai kuma abin da mutum ya yi wa ‘yan’uwansa mutane, wannan hakki sai dai a biya masu hakkinsu kafin a nemi gafararsu, idan sun ga dama su yafe maka.
Tuban Gwamna Ganduje Ya Zo A Lokacin Da Ba Za A Karbar Ba – Ata
Tsohon shugaban Kasuwar Kantin Kwari Sanusi Umar Ata, da yake tsokaci kan neman gafarar da Gwamna Ganduje ya nema daga Kanawa, ya bayyana cewa gaskiya magana idan aka dubi ayar Alkur’ani da ke cewa, “Babu tuba ga wanda ya zo gargarar mutuwa,” wannan tuba da Ganduje ke nema bai wuce ganin damar da Allah ya ba shi ta zo karshe ba, don haka dole ya nemi wannan gafara.
Ya ci gaba da cewa duk cikin wadanda Allah ya bai wa damar mulkar Jihar Kano babu wanda ya fi Ganduje samun dama, amma bai amfani da damar wajen tausasa wa jama’a ba. Misali, ya yi taro da ‘yan a caba yake fada masu cewar tsiyar Nasara sai za shi gida, yanzun ya kama hanyar tafiya gidan kenan? Haka kuma an ji shi a wani taro yana cewa zai hau dutsen Goron Dutse ya tsinke birki ya gangaro da gudu, kenan zai murkushe kowa? Haka kuma ya ce zai dau manjagara ya sosa bayansa da shi, kenan akwai tanadin keta a zuciyarsa.
“Saboda haka mu aganinmu, wannan kawai bai wuce gargarar kubucewar mulki ba, muna ganin batun neman gafarar talakawan Kano lokaci ya kure masa,” in ji Ata.
Neman Gafarar Ganduje Rufo Kura Da Bargon Akuya Ne Kawai – Kwamared Ishak
Wani mai fashin bakin a kan harkokin siyasar Jihar Kano, Kwamared Ishak Gandun Albasa ya bayyana neman gafarar da Ganduje ya yi da cewa wayon rufo kura da bargon akuya ne kawai.
A cewarsa, ba zai yiwu shugaban da ya riki jagorancin al’umma na tsawon shekaru takwas ya fito ya ce yana neman jama’ar jihar su yafe masa abin da ya yi masu ba. idan a matsayinsa na Dan’adam ne yake neman wannan gafara kan abin da ya aikata da kuskure, wannan wata magana ce daban, amma idan ya san yana neman gafara ne kan ta’asar da ya yi wa jama’ar Kano, wannan kuma hakki ne da ya kama ya dawo masu da kayansu, sai a wuce wurin.
“Kasancewar Dan’adam mai kuskure ne, hakan ba yana nufin ka ci dukiyar al’umma ko ka yi wasarai-rai da dukiyarsu ka buda baki su ka ce su yafe maka. Abin da ya kamata shi ne, idan hakkinsu ka cinye ko ka bayar da dama aka ciniye, sai da dawo masu da wannan hakkin, idan kuma wani kuskure ne ya yi wanda kowani Dan’adam na iya yin irin wannan kuskuren, wannan ba laifi idan ya nemi gafara, amma ban da abin da aka yi wa jama’a da ganganci,” in ji Kwamared Ishak.
Neman Gafarar Ganduje Ya Nuna Cikar Dattijantakarsa – Amb. Dandago
Amb. Mansur Haruna Dandago, dan Kasuwa kuma dan siyasa ya bayyana cewa neman gafarar da Gwamna Ganduje ya yi shi ne abin da ya kamata ga duk wani dattijon arziki, kuma wannan ke tabbatar da sunansa na Khadimul Islam, ganin yadda Allah ya ba shi damar jagorantar Kanawa tsawon shekara takwas, ya gode wa Allah bisa wannan bai wa, sannan kuma ya nemi gafarar wadanda ya sabawa, shi kuma a kashin kansa ya tabbatar da yafe wa kowa.
“Babu shakka mun yafe masa, kuma Allah ya yafe mana baki daya.
“Gwamna Ganduje shi ne mutun na farko daga cikin wadanda suka jagoranci Kanawa a matsayin gwamna wanda ya nuna wannan dattijantaka na neman gafarar wadanda ya mulka. Shi ma Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero shi ma a lokacin da ya cika shekara 50 a kan karagar mulki ya nemi gafarar al’ummar Jihar Kano, don haka wannan kyakkyawna misali ne ga duk mai neman haduwa da Allah lami lafiya,” in ji Amb. Dandago.