Idan matsalan ‘Infection’ ya kai wani lokaci a jikin mace sai wani farin ruwa ya fara fito mata mai kalar Kindirmo ko kuma koko, yana da karni har ya rika damunta:
Yawan ciwon mara, ko jin motsi a maran, kaikayin gaba mai tsanani, Jinzafi lokacin fitsari, Jin zafi lokacin wani abu haka, Bushewar gaba ko kuma ta ji ta ba daidai ba, Ciwon baya ko kuma ciwo a gefe, Fesowar kuraje a gaba da sauran su.
Duk wadannan suna daga cikin alamu da suke nuna cewa kina dauke da cutar ciwon sanyi, sannan a wani lokacin wannan matsalar ta ciwon sanyi yana komawa ya kama maigida har ya haifar masa da kuraje ko kuma tsatstsagewar gabansa yana yi masa ciwo, saboda haka sai su rika yin amfani da maganin ciwon sanyi tare domin saurin biyan bukata.
Ina masu fama da cutar sanyin mara, sanyin ciki, sanyin fata, sanyin kashi, sanyin bandaki da sauran cututtuka masu alaka da sanyi?
Abubuwan bukata:
Tafarnuwa, Kanunfari, Kurkum, Citta danya, Kajiji, Kimba, Bagaruwa, Masoro, Aiden fruit, Cinnamon sticks, Lemon tsami, Ruwa Lita 6
Yadda za a hada:
Hade su ake yi a tafasa a rika sha kofi daya safe da yamma na kwanaki bakwai, In sha Allah za a samu lafiya. A kiyaye
Ban da maza marasa aure, Ban da mata masu ciki, Ban da masu Olsar da ta yi tsanani.