Masana sun yi bayanin abubuwa da yawa masu hana samun ciki. Amma ga guda uku masu muhimmanci za mu yi bayaninsu: da kuma maganin da ya dace.
1. Zafin mahaifa:
Wannan matsala idan ta yi yawa a cikin mahaifa tana iya sanya abu idan ya shiga ciki sai zafin ya yi mata yawa sai ya rube, domin abin yana kasancewa a cikin mahaifa kwana 40 kamar yadda ya tabbata cikin hadisi Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Hakika dayanku ana hada halittarsa a cikin mahaifiyarsa kwana
40 yana digon maniyyi, sannan ya koma gudan jini misalin kwana 40, sannan ya koma tsoka kwana 40”. sadaka Rasulullahi (S.A.W).
Idan maniyyi ya shiga cikin mahaifa wannan zafin madaidaici shi zai fara dukansa sai ya fara zama kamar jini-jini zuwa kwana 40, sai ya daskare ya zama tsoka, idan mahaifar mace tana da zafi da yawa kafin kwana 40, sai zafin ya yi masa yawa sai ya rube. Ka ga ciki ba zai samu ba.
Alamomin wannan cuta ta zafin Mahaifa ita ce:
1) Ciwon mara mai daurewa (2) Wasan al’ada (3) Ganin jinı dunkule-dunkule lokacin al’ada.
Yadda za a magance:
Sai ki nemi Sanya da Shammar da Albabinaj da Zuma sai ki tafasa su sannan ki riga sha sau uku a rana.
2. Matsala ta biyu sanyin Mahaifa:
Wannan shi ne ake ce masa sanyin mahaifa. Shi ne idan abu ya shiga cikin mahaifar sai sanyi yaí masa yawa sai ya kasance ya fi yadda ake bukata saboda haka ciki ba zai samu ba donmin yana zarce kwana arba’in yana matsayin maniyyi bai koma jini ba, don haka ciki ba zai samuba.
Alamun sanyi mai hana haihuwa
1- Fitar farin ruwa ta gaba. 2- Warin gaba 3- Kaikayin gaba. 4- Daukewar sha’awa. 5- Jin motsi a ciki.
Yadda za a magance shi:
A samu Tafarmuwa gwangwani daya, Ridi gwangwani biyu. Kanunfari cokali biyu. jan algarif gwangwani daya a daka a rika dafawa ana sha kamar shayi sau 3 a rana
3. Matsala ta uku
Namijin dare: Shi ne wani aljani da yake iya aurar budurwa ko matar aure. Yana hana budurwa aure. Ita kuma matar aure ya hana ta haihuwa ko hana ta zaman lafiya da miji. Alamunsa sun hada da:
1- Mafarkin jarirai. 2- Mafarkin wani na saduwa dake. 3- Bacin rai da faduwar gaba. 4- Mafarkin ruwa. 5- Yawan ciwon kai. 6- Jin motsi a cikin ciki kamar kina da ciki, sai an yi (scanning) a ce miki babu komai a ciki. 7 Idan budurwace da maganar aurenta ya taso sai ya lalace.
8- yawan Damuwa da rama ko Kiba mara misali Wannan sune kadan daga cikin alamun namijin dare.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp