• English
  • Business News
Wednesday, October 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ko Kin San… Warin Gaba Da Yadda Za A Magance

by Bilkisu Tijjani
1 year ago
Warin gaba

Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ko Kin San.

A yau shafin namu yana zai karkata akalarsa ne kan abin da ke kawo warin gaba.

Ya kamata kowace mace ta san muhimmancin amfani da Auduga mai laushi saboda yadda yake samar wa wacce take da lalaurar waring aba gaba iska kuma yana yin kyakkyawan aiki wurin kawar da gumi da ruwa daga jikinku. Yawan danshi zai iya sa ki kamu da kwayoyin cuta da za su yi wa gabanki illa.

Sannan ya kamata ki kula da yawan sauya kamfai da siket saboda idan suka yi datti kuma kika maimaita su to akwai yiwuwar su haifar da warin gaba.

Sanin lokacin ganin likita
Idan wannan warin yana tare da alamun da ba ku saba gani ko ji ba, ya kamata ku guji yin magani a gida ku tuntubi likitoci.
Misali: Idan warin gaba ya fi na al’ada karfi kuma kin lura cewa yana kara karfi, to kina bukatar ganin likita.

LABARAI MASU NASABA

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

Gwamnonin Arewa Sun Amince Da Kafa Ƴansandan Jihohi: Ko Hakan Zai Yi Tasiri Ga Sha’anin Tsaro?

Haka nan, idan kin ji gabanki ya fara wari kamar na “kifi” wannan ma ya kamata ki yi saurin ganin likita. Wari mara kyau alama ce ta kamuwa da cutar gaba. Ba za ku so ku jinkirta magance matsalar ba domin cutar gaban da ba a nemi maganinta ba kan iya jawo matsalar rashin haihuwa idan ta dade ana fama da ita.

Wani ruwa da ke fitowa daga gaban mace na iya zama na ka’ida. Idan kin lura da canji a launin ruwan, misali launin da kika saba gani fari ne ko bai da kala amma sai kika fara ganin wani launin daban, to zai iya yiwuwa kin kamu da cuta.

Yawanci kaikayin al’aura ba matsala ba ce, amma idan kika fara jin kaikayin ya fara yawa ko kuma ya fara zafi da radadi, to alama ce na babbar matsala.

Hanyar magance sake warin gaba:
Da zarar kin kawar da warin gaba wanda ba a saba ji ba, to ki kiyaye wadannan shawarwari don hana wata matsalar:
Kula da cin lafiyayyen abinci mai sinadiran gina jiki. Yawaita cin ‘ya’yan itace, da kayan lambu. Daidaitaccen abinci yana samar da lafiyayyen jiki, kuma hakan ya hada da gabanki.

Kasance mai yawan shan ruwa. Shan ruwa mai yawa yana da amfani sosai a dukkan jiki ba sai ga fata ba kawai. Yana iya taimaka wa ga lafiyar gabanki, kuma ta hanyar karfafa gumi mai kyau.

Ki dinga wanke gabanki kafin saduwa da kuma bayan saduwa. Jima’i kan iya kawo yaduwar kwayoyin cuta, da kuma abubuwan kamar man shafawa da maniyyi daga kwaroron roba.

Ku daina amfani da matsattsun kaya. Tufafi masu matsewa ba sa barin gabanku ya sha iska. Samun isasshiyar iskar na da muhimmanci ga lafiyar gaban mace.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)
Uwargida Sarautar Mata

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

October 12, 2025
Gwamnonin Arewa Sun Amince Da Kafa Ƴansandan Jihohi: Ko Hakan Zai Yi Tasiri Ga Sha’anin Tsaro?
Uwargida Sarautar Mata

Gwamnonin Arewa Sun Amince Da Kafa Ƴansandan Jihohi: Ko Hakan Zai Yi Tasiri Ga Sha’anin Tsaro?

September 12, 2025
aure
Uwargida Sarautar Mata

Ko Kin San… Matsalolin Mahaifa Da Suke Hana Haihuwa 

July 27, 2025
Next Post
Ministan Kudin Zimbabwe Ya Jinjinawa Gudummawar Masu Zuba Jari Daga Sin

Ministan Kudin Zimbabwe Ya Jinjinawa Gudummawar Masu Zuba Jari Daga Sin

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

October 14, 2025
Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani

Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani

October 14, 2025
Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria 

Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria 

October 14, 2025
Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa 

Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa 

October 14, 2025
Kotu

Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta

October 14, 2025
Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin

Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin

October 14, 2025
Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya

Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya

October 14, 2025
Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo

Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo

October 14, 2025
Asuu

An Janye Wajibcin Samun Kiredit A Darasin Lissafi Ga Ɗaliban Fannin Zamantakewa Don Shiga Manyan Makarantu 

October 14, 2025
Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata

Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata

October 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.