Duba da yanayin yadda tarihin siyasar Nijeriya ke tafiya a iya cewa maza ne suka yi kaka-gida tare da mamaye manyan guraben siyasa, inda kuwa aka bar mata da sidin ludayi, ma’ana an bar su da rikon kananan mukamai.
Sai dai a baya-bayan nan abubuwa sun fara tafiyar hawainiya, inda kidan ya fara sauya-hakan ya sa ita ma rawar ta fara sauyawa.
Abun mamaki shi ne mata da dama sun yi bajinta tare da taka rawar gani a bangarori daban-daban na rayuwa, amma babu wadda ta taba zama shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, shugaban majalisar dattawa, sai dai Olubunmi Patricia Etteh wadda ita kadai ce ta taba zama kakakin majalisar wakilai a shekarar 2007. Ita ma an tsige ta daga mukamin kan wasu zarge-zarge da ke da alaka da almundahanar kudade a wancan lokaci.
Dame Birginia Ngozi Etiaba ta sauya wannan tarihi a shekarar 2006 lokacin da ta zama mukaddashiyar gwamna ta farko a Nijeriya bayan tsige Peter Obi a matsayin gwamnan Jihar Anambra, bisa zarginsa da sama da fadi da kudaden jihar. Sai dai abun takaici ba ta wuce watanni uku ba, wata kotu ta sake mayar da Obi a matsayin gwamnan Jihar a 2007.
Tun daga wannan lokaci mata da dama sun yi gwagwarmaya sosai kan cewar sun shiga cikin tafiyar an dama da su amma da yawansu hakarau ba ta cimma ruwa ba.
Ministar Al’amuran Mata ta ta yanzu, Pauline Tallen ta taba rike mukamin mataimakiyar gwamnan Jihar Filato kuma ta nuna sha’awar yin takara amma ta yi rashin nasara a hannun Jonah Jang. Ita kuma Hajiya Aisha Jummai Alasan, wadda aka fi sani sa Maman Taraba ta samu tikitin takarar gwamnan Jihar a 2015 amma Dariu Ishaku ya maka ta a kotu, inda aka kwace takarar aka ba shi a kotun koli.
Sai dai wannan tarihi na yadda siyasar Nijeriya ke tafiya, musamman yadda maza suka yi kaka-gida ba ta sa mata sun karaya, hasali ma wasu sun sake dukan kirji sun sake fitowa don a kara da su a babban zaben 2023 da ke tafe.
Fitacciya daga cikin wadannan mata da suka yi ta maza ita ce Sanata Aishatu Ahmad Dahiru, wadda aka fi sani da Binani, wadda ita kadai ce mace mai rike da tikitin takarar daga cikin manyan jam’iyyun siyasar kasar nan.
Binani ta kada tsohon shugaban hukumar EFCC na kasa, Nubu Ribadu da tsohon gwamnan Jihar Adamawa Jibrilla Bindow, inda ta lashe zaben fidda gwanin da APC ta gudanar a shekarar da ta gabata.
Yanzu haka dai Binani ce ‘yar takarar gwamnan Jihar Adamawa a jam’iyyar APC kuma za ta kara da gwamnan Jihar mai ci a yanzu na jam’iyyar PDP, Ahmadu Fintri a zaben da za a gudanar a watan Maris, 2023.
Akwai kuma Nnenna Lancaster-Okoro wadda ita ma ta kasance mace ‘yar takarar gwamnan Jihar Abia a karkashin jam’iyyar PRP. Bayan ita akwai irin su Ngozi Ogbuleke daga Jihar Abia a jam’iyyar SDP, Beatrice Itubo daga Jihar Ribas a jam’iyyar NLC, Hajiya Khadijat Abdullahi-Iya daga Jihar Neja a karkashin jam’iyyar APGA, akwai Kasim Jackie-Adunni daga Jihar Ogun a jam’iyyar NNPP.
Ragowar sun hada da Obiang Marikane Stanley daga Jihar Ribas a jam’iyyar ADP, Sophia Cookey daga Jihar Ribas a jam’iyyar ZLP, Tina Barde daga jam’iyyar LP a Jihar Neja, sai kuma Iskil-Ogunyomi Sufiat Olajogun Adekemi daga jam’iyyar AA daga Jihar Ogun.
Duk irin sakamakon da ya faru a watan Fabrairun 2023, matan Nijeriya sun taka rawar azo a gani ta hanyar nuna sha’awarsu ga yadda ake gudanar da harkokin siyasa da yadda ake gudanar da mulkin kasar nan. 2023 za ta zama wani tsani kan yadda makomar siyasar mata za ta kasance a gaba.
A cikin shirinmu mai taken ‘Madubin Rayuwa’ da LEADERSHIP Hausa ke gabatarwa a Manhajar Twitter Space, wanda Maryam Rabiu da Rukayya Sadauki suka gabatar kwanan nan, ya yi duba da dauraya kan yadda wannan tafiya ta siyasa ta mata za ta kafa sabon tarihi a 2023.
A cikin shirin an gayyaci Zahra Danejo, Ibrahim H. Abdulrahman, Tijjani Abdullahi da kuma Malam Abdullahi Utako wadanda suka yi fashin baki kan yadda suke ganin yadda takarar Aisha Binani za ta iya sauya fasalin siyasar mata a 2023.
Daya daga cikin bakin da suka yi fashin baki, wato Zahra Danejo lauya ce, ‘yar siyasa, ‘yar gwagwarmaya sannan daya daga cikin mata masu ruwa da tsaki daga cikin kwamitin yakin neman zaben Aisha Binani a Jihar Adamawa, ta bayyana irin tashi-fadin da Binani ta yi har ta zo matakin da ta ke a yanzu.
“Mu a Adamawa mun riga mun yi nisa domin har mun karbi tutar takara, mun ci zaben fidda gwani na gwamna. A halin da muke ciki yanzu ‘yar takararmu na daga cikin wadanda ake ganin za su takara rawar gani a zaben da za a yi a watan Maris.
“Mu a Adamawa ba abin da zamu ce sai godiya kawai, saboda abin da mutane da dama ke ganin ba faru ba, abubuwan da ake fada mana ba zai yiwu ba sun ma riga sun faru an wuce wajen. Don haka mu yanzu muna shirin yadda zamu yi yakin neman kuri’u a babban zaben da ke tafe.
“Wani abun alfahari shi ne wannan abun ana sa rai sai faru ne a Arewa, a jihar Arewa, wato mace Musulma, Bafulatana na shirin zama gwamna,” in ji ta.
Zahra Danejo ta bayyana irin yadda Aisha Jummai Alasan ta shimfida tubalin tafiyar siyasar Binani.
“Tabbas Maman Taraba ce ta fara namijin kokari tare sa yin gangami mai girman gaske, kuma ita ta sharewa Binani hanya don yi tafiya.
“Wato Jummai Alasan ce ra fara rarrafe sai Aisha Binani ta fara tafiya.”
Danejo ta ce duba da kusancinta da Binani ta gano ire-iren kalubale da ta fuskanta a matsayinta na mace lokacin da ta fito neman takarar kujerar gwamnan Adammawa.
“Gaskiya mu a lokacin yakin neman zabe ba mu fuskanci wani kalubale wanda ke da alaka da jinsi ba, abin da muka fuskanta shi ne mun zauna da wasu mutane sa ba su yarda da mu ba, mu ma ba mu yarda da su ba.
“Amma kuma wasu sun kalli jinsinta kamar wani lahani. Wato zaka ji mutane na fadar abubuwan alheri da ta yi da sauransu amma ana yin magana za ka ji sun ce mace ce.
“Amma Alhamdulilah da yake ita mutum ce da ta dade tana yi wa mutane alheri kuma ta dade tana yi wa mutane hidima da yawa ba su duba wannan ba, gani suke idan aka ba ta dama alherinta zai karu.
“Amma wasu ‘yan siyasa musamman saga jihohin Kano, Kaduna da sauransu zaka ji suna ku ya za a yi ku bari mace ta mulke ku kuna maza, da dai maganganu marasa kan gado haka,” in ji Danejo.
“Amma duk da wadancan maganganu na tsangwama ba mu rasa goyon baya ba musamman na mutanen Jihar Adamawa domin su ne wadanda za su zabe mu.
“Akwai abin da nake son jan hankalin mutane, duk wannan surutu da ake yi mata ne masu zabe, su ne suke fita su kada kuri’a a lokacin zabe; da ciki da goyo da mene ne za su fito a ranar zabe su yi zabe.
“Akwai wani gyara da aka yi a kundin tsarin jam’iyyarmu wanda ya ce dole a samu mata akalla guda biyu a kowane mataki tun daga mazaba na jam’iyyar wanda shi ne ya taimake mu a zaben fidda gwani. Kuma ita mace ita ta san ciwon ‘ya mace, ita ta san gwagwarmayar mace.”
Shi ma Arewa Twitter wanda yana daya daga cikin manyan bakin ya bayyana nasa ra’ayin kan yadda yake ganin tafiyar takarar Banani.
“Abun duba a nan shi ne tsarin da kasar nan ke tafiya ba tsarin addini bane, amma a matsayinta na mace za a karbe ta musamman duba da yadda wasu tanade-tanade na rayuwar mutanen Arewa ke tafiya.”
A cikin shirin mutane da daban-daban sun bayyana ra’ayinsu kan takararta a matsayinta na mace. Wasu sun tafi a kan cewar lallai akwai bukatar maza su ja ragamar mulki, duba da irin hikima da gogewa da suke da ita na rayuwa da kuma irin yadda suke shan gwagwarmaya wajen jure damuwa da wahalhalunbda za su fuskanta.
Kazalika, sun sake bayyana cewar namiji ne ke da taurin zuciya da iya cijewa akan magana daya ko da kuwa zai fuskanci kalubale da suka daga abokan hamayya.
Yayin da suke ce mace na da taushin zuciya da sanyi a lokuta da dama, wanda a cewarsu hakan na iya zame mata koma baya idan ta zama gwamna a lokacin tafiyar da sha’anin mulkinta.
Wasu kuma sun danganta takarar ta Binani a matsayin wani bigire da ya sabawa tsarin Addinin Musulunci. Har wa yau, suna ganin cewar Al’ada irin ta rayuwar Bahaushe na da tsari wanda bai baiwa mace kofa don ta yi shugabanci ba.
Sai dai ko mene ne, wannan zabe da za a shiga wata ‘yar manuniya ce da za ta fayyace makomar siyasar mata a wannan kasa a nan gaba.