A shekarar nan ta 2025 ne ake cikar shekaru 100 da bullar fannin ilimin “Quantum Mechanics”, kana shekara ce ta kimiyya da fasaha ta “quantum” ta duniya. Sai dai kuma a farkon shekarar ta bana ne gwamnatin Amurka ta fara aiki da sabuwar dokar hana daidaikun mutane da kamfanoninta, su zuba jari a wasu fannonin da suka shafi fasahohin zamani da kasar Sin take da su, ciki har da lissafin “Quantum Computing”.
A matsayinsu na manyan kasashe masu karfin kimiyya da fasaha guda biyu a duniya, Sin da Amurka suna taka rawa a manyan fannonin dake shafar kimiyya da fasahar quantum. A halin yanzu, Amurka na kara yin takara tare da kasar Sin, musamman a bangaren kimiyya da fasaha ta zamani. Kuma Amurka ta fara aiwatar da sabuwar dokar bisa abun da ta kira “tsaron kasa”, da zummar kara taka birki ga ci gaban kasar Sin a bangaren kimiyya da fasaha ta zamani, da kawo cikas ga karfin yin takara na kasar, al’amarin da ya shaida damuwar ’yan siyasar Amurka kan saurin bunkasar kimiyya da fasaha ta kasar Sin.
- Me Amurka Ta Kawowa Duniya A Shekarar 2024?
- Shekarau Ga PDP: A Bai Wa Matasa Damar Rike Madafun Iko A 2027
Kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na Sin da Amurka, zarafi ne ga kowa, a maimakon cin nasara daga faduwar wani bangare. Kasashen Sin da Amurka na kan muhimmiyar gaba a duniya, a fannonin kimiyya da fasaha ta zamani, ciki har da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI, da binciken sararin samaniya da sauransu, kuma inganta hadin-gwiwarsu, ba taimakawa ci gaban kimiyya da fasaha da tattalin arziki da zaman rayuwar al’ummarsu kawai zai yi ba, har ma zai yi amfani wajen tinkarar kalubalolin dukkanin fadin duniya, da habaka tattalin arzikin sassan kasa da kasa, da kuma kara samar da alfanu ga al’ummun duniya, wanda hakan al’amari ne da ya kasance nauyi na musamman dake rataye a wuyan Sin da Amurka.
Za’a kafa sabuwar gwamnatin Amurka nan da rabin wata mai zuwa. Fatan shi ne Amurka za ta kalli hadin-gwiwar Sin da Amurka a bangaren kimiyya da fasaha yadda ya kamata, ta gyara kura-kuran da ta aikata, da hada kai tare da kasar Sin, ta yadda nasarorin hadin-gwiwarsu a fannonin kimiyya da fasaha za su amfani kasashen biyu, gami da duk fadin duniya baki daya. (Murtala Zhang)