A kwanakin baya, na zanta da wasu masana a yayin wani taro da ya gudana a birnin Beijing, karkashin laimar dandalin masanan Sin da Afirka, inda kalaman da wani masani dan kasar Habasha mai suna Yonas Adaye ya yi, ya burge ni matuka.
Ya ce, “sakamakon bambancin al’adu da tarihi, ba za samu wani tsarin raya kasa da zai biya bukatun dukkan kasashe ba. Wasu kasashen yamma na ganin cewa, ‘Ba za a samu nasarar tafiyar da harkokin mulki ba, idan ba a rungumi tsarinmu ba.’
Amma kasashen Afirka ba za su ci gaba da amincewa da ra’ayinsu ba.” Na yarda da ra’ayin masanin. Saboda idan muka nazarci fasahohin da kasar Sin ta samu, to, dole ne duk wata kasa mai tasowa ta yi kokarin bin turbar raya kasa ta kanta, kafin ta iya samun ci gaba mai dorewa.
Tun bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949, kasar ta nace da zama karkashin mulkin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da turbar tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta Sin. Hakan a ganin kasashen yamma, wai “mulkin kama karya” ne. Sai dai sakamakon da kasar Sin ta samu karkashin turbar da ta tsara da kanta, shi ne ya haifar da ci gaban tattalin arzikinta.
Wanimasani a kasar Afirka ya taba bayyana cewa, “ Jimillar GDPn kasar Kenya ta fi ta kasar Sin yawa, a shekarar 1961. Amma zuwa shekarar 2020, GDPn Kenya ya karu da ninki 3, yayin da jimillar ta kasar Sin ta karu da ninki 50.” Kalamansa sun shaida cewa, turbar da kasar Sin ta zaba, ita ce daidai.
Cikin shekaru 5 da suka wuce, duniyarmu ta yi fama da koma bayan tattalin arziki. Inda aka fuskanci tarin kalubaloli, da tsanantar rikici tsakanin wasu kasashe, ko tsakanin al’ummomin wata kasa.
Amma kasar Sin tana bin hanyarta ta neman ci gaba yadda ya kamata. Wasu abubuwan da na gani da ido su ne: Mazauna kauyuka sun samu wadata ta hanyar raya harkar yawon shakatawa, ko kuma tallata amfanin gona ta kafar Internet.
Yayin da a cikin birane, ana samun karin itatuwa da bishiyoyi, da kyautatuwar muhallin zama. Kana ‘yan saman jannatin kasar Sin suna zirga-zirga a sararin samaniya ta cikin kumbunan kasar.
Ban da wannan kuma, kasar ta yi nasarar shawo kan yaduwar cutar COVID-19, da maido da ayyuka masu alaka da tattalin arziki cikin sauri. Haka zalika, a yankin Hong Kong na kasar, kasar Amurka ta ci tura a yunkurin na ta da tarzoma, da juyin juya hali, inda aka maido da kwanciyar hankali a yankin, bisa matakan shari’a da kasar Sin ta dauka.
Ban da wannan kuma, na ga yadda kasar Sin ta iya kare cikakkun yankunanta daga kasar da take nuna fin karfi a duniya. Kana abu mai muhimmanci shi ne, na ga yadda Sinawa suke nuna cikakken imani kan turbarsu, inda ko da yake suna kokarin tinkarar matakan wasu kasashe na neman shafawa kasar Sin bakin fenti, da hana ta samun ci gaba, a hannu guda kuma suna nacewa kan akidar al’ummar dan Adam mai makomar bai daya, da hadin gwiwa don moriyar dukkan bangarori.
Hausawa su kan ce, “Ko wace kwarya tana da abokin burminta”, kana “ Kayan aro ba ya rufe katara.” Idan mun ce kasar Sin na da wani asiri na raya kai, to wannan shi ne zabin turbar da ta dace da yanayin kasa, da kokarin tabbatar da kwanciyar hankali, gami da raya tattalin arziki.
Idan al’ummar wata kasa suna iya kiyaye wani yanayi na hadin kai da juna, a kokarin raya kasarsu, ba tare da ta da zaune-tsaye ba, to, duk wani kalubale, ba zai iya hana kasar samun ci gaba ba. (Bello Wang)