Tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya ce, magajin kujerarsa Shugaba Bola Tinubu, yana taka rawar gani sosai tun bayan hawansa mulki watanni tara da suka gabata zuwa yanzu.
Tsohon shugaban kasar ya ce, Tinubu ya taka rawar gani idan aka yi la’akari da yanayin da ake ciki, sai dai ya tabbatar da cewa Nijeriya wata kasa ce mai sarkakiya wajen gudanar da mulki.
- Ku Yi Haƙuri Da Gwamnatin Tinubu – Shettima
- Ƙudurin Tinubu Na Samar Da Abinci Ba Faɗe A Fatar Baki Ba Ne Kaɗai, Gaskiya Ne – Minista
Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban hukumar kwastam, Bashir Adewale Adeniyi da jami’an gudanarwar hukumar a garin Daura na jihar Katsina a karshen mako da muka yi bankwana da shi.
Tinubu ya fuskanci suka sosai kan wasu manufofinsa na tattalin arziki da suka hada da cire tallafin man fetur da lamuran da suka shafi hada-hadar canjin kudi.
Wadannan tsare-tsare da wasun su sun haifar da hauhawar farashin kayayyaki da tabarbarewar tattalin arziki da faduwar darajar Naira, wanda a ‘yan kwanakin nan ya haifar da zanga-zanga a fadin kasar.
Yayin da yake jawabi a lokacin ziyarar, Adeniyi da tawagarsa, Buhari ya ce Nijeriya na da wahala wajen gudanar da mukin kasar, ya bukaci ‘yan kasar da su jure wa matsalolin tattalin arziki da ake fama da su a kasar, tare da marawa manufofi da shirye-shiryen gwamnati mai ci.
Adeniyi, a nasa jawabin, ya godewa tsohon shugaban kasar kan rawar da ya taka wadda ba a taba ganin irinta ba wajen tallafawa dokar NCS ta 2023.