Ranar Laraba 15 ga watan Mayun kowace shekara, ranar ce ta tunawa da abin da ya faru ga Palasdinawa a lokacin yakin gabas ta tsakiya na farko a shekarar 1948. A shekaru 76 da suka gabata, sama da rabin Palasdinawa sun gudu ko an kore su daga gidajensu sakamakon yakin da ya faru tsakanin Larabawa da Yahudawa, inda da yawa daga cikinsu har da zuriyoyinsu suka zama ‘yan gudun hijira a zirin Gaza.
Amma har zuwa yanzu, ba a daidaita wannan kuskure ba, inda Palasdinawa ke ci gaba da fama da mawuyancin hali, kuma yanayin da suke ciki na kara tsananta. Abun tambaya a nan shi ne ko yaushe ne za a kai ga ganin karshen wahalhalun ga Palasdinawa?
- An Kaddamar Da Bikin Nuna Kayayyakin Fasahohin Al’adu Masu Alaka Da Gasar Olympics A Shanghai Na Sin
- Hare-hare A Kan Rafah: Amurka Ta Dakatar Da Tura Wa Isra’ila Bama-bamai
Kudurin kwamitin sulhu na MDD mai lamba 242, hanya ce mafi dacewa ta warware wannan matsala, wato kafa kasar Palasdinu dake da ‘yancin kai da cikakken ikon mulki mai hedkwata a gabashin birnin Kudus, bisa iyakar da aka shata a shekarar 1967.
Sin tana kokarin hadin gwiwa da kasashen duniya don tabbatar da manufar kafa kasashe biyu, ta yadda Palasdinawa za su kafa kasarsu mai ‘yancin kai. Sai dai ba za a kai ga kawo karshen mawuyacin halin da Palasdinawa ke ciki da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin bangarorin biyu ba, har sai kasashen duniya sun yi iyakacin kokarin hadin kai da juna, don gaggauta shawarwarin wanzar da zaman lafiya tsakanin Palasdinu da Isra’ila, da ma tabbatar da manufar samar da kasashe biyu. (Mai zana da rubuta: MINA)