Tun bayan cikar burin shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na kawo dan wasa Kylian Mbappe, rahotanni da masu sharhi suka fara bayyana cewa magoya baya da shugabannin kungiyar za su karkatar da soyayyar da suke yi wa Jude Bellingham zuwa Mbappe, matakin da kociyan kungiyar, Carlo Ancelotti ya bayyana a matsayin shaci fadi kuma matsayin Bellingham a Real Madrid ba zai canza ba a bana, bayan daukar Kylian Mbappe.
Bellingham, dan wasan Ingila, mai shekara 21, ya taka rawar gani a Sifaniya a kakarsa ta farko, wanda ya zura kwallo 23 a wasanni 42 kuma yana cikin ‘‘yan wasan da suka taka rawar gani a Real Madrid, wacce ta lashe La Liga da Champions League a kakar da ta wuce.
- Muna Samun Nasarori A Yaki Da Gurbatattun Masana’antar Kannywood – Tijjani Asase
- Matasa Sun Yi Warwason Motar Taki A Adamawa
Mbappe, kyaftin din tawagar Faransa, mai shekara 25, ya koma Real Madrid a bana daga Paris St Ger-main, bayan da kwantiraginsa ya kare a watan Yuni kuma tuni ya koma Real Madrid bayan kammala gasar cin kofin Nahiyar Turai.
Ancelotti ya yi watsi da batun cewa Bellingham ba zai dinga buga gurbin da ya saba bugawa a Real Ma-drid ba, domin bai wa Mbappe dama, kociyan dan kasar Italiya ya bayyana cewa babu wani abu da zai canza a gare shi.
“Kakar farko, ya bai wa mutane mamaki, saboda yadda ya nuna kwarewa, yanzu kuma ya kara samun gogewa. Kenan wannan kakar haka zai ci gaba da taka rawar gani kuma zai ci gaba da zama fitatcen dan wasan wannan kungiya, wanda zai ci gaba da taka rawar da kungiyar za ta ci gaba da samun nasarori,” in ji Ancelotti
Ancelotti ya goyi da bayan Bellingham, wanda aka rika sukar kwazonsa a Euro 2024, duk da cewar Ingila ta kai wasan karshe a gasar kuma ya ce wannan ra’ayinsa ne, amma Bellingham ya taka rawar gani sosai a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Euro 2024.
Sai dai ba iya shugabannin Real Madrid ba ne ake ganin za su mayar da Mbappe dan lele, magoya bayan kungiyar ma ana ganin za su karkata ga Mbappe, kasancewar sun dade suna fatan ganin ya koma kungiyar.
Amma ana ganin ba iya Bellingham da Mbappe bane za a samu wannan cece kucen, dan wasa Binicius ma ana ganin yana bukatar goyon bayan magoya baya da shugabanni saboda nauyin da yake kansa a kungiyar a yanzu.