Kocin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Abdallah Usman zai jagoranci kungiyar a karon farko cikin makonni 5 a wasan da Pillars zasu kara da Haertland Owerri.
Wasan na mako 32 a gasar Firimiya ta Nijeriya da za a buga a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a birnin Kano, zai zama wani mataki da Abdallah zai sake kwantar da hankalin magoya bayan ƙungiyar bayan hatsaniyar da su ka samu a ƙarshen watan Fabrairu.
- Me Dakatarwar Da Pillars Ta Yi Wa Usman Abdalla Ke Nufi?
- Kano Pillars Ta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Kocinta, Usman Abdallah
Pillars na mataki na 8 da maki 44 a wasa 31 da su ka buga, yayinda Heartland Owerri ke matsayi na 18 da maki 35 a wasanni 31.
Nasara a gida zai sa Pillars ta sake samun damar buga gasar Confederation Cup, amma kuma rashin nasara zai sake nitsar da kungiyar da kuma fargabar yin biyu babu a wannan kakar wasannin sakamakon wasanni 7 kacal su ka rage.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp