Ƙungiyar masana fasahar fata da na kimiyyar sinadarai ta Nijeriya ta damu matuƙa da haɗewar Cibiyar Fasahar Fata da Kimiyya ta Nijeriya (NILEST) da kuma Cibiyar Bincike Kan kimiyyar Sinadarai (NARICT), inda ta bayyana cewa hakan babbar barazana ce ga jin daɗi da walwalar masu gudanarwa.
Idan za a iya tunawa batun haɗewar ma’aikatu da hukumomin gwamnati ya zama ruwan dare tun bayan fitar da rahoton Oronsanye game da sauye-sauyen ayyukan gwamnati sama da shekaru goma sha biyu da suka gabata.
- ‘Yan Bindiga Sun Tarwatsa Kauyuka 10 A Jihar Kaduna
- Pogba Zai Ɗaukaka Ƙara A Kan Dakatar Da Shi Daga Buga Ƙwallo Na Tsawon Shekaru 4
Ana ɗaukar wannan matakin a matsayin wata dabara da gwamnati ta ɓullo da shi domin rage kuɗaɗen da ƙasa ke kashewa wajen gudanar da ayyukan gwamnati. Sauran dalilan haɗewar sun haɗa da; kawar da tsarin rashin gudanarwa, maimaita ayyuka, kwaikwayo, da sake fasalin ayyukan gwamnati wanda zai inganta yanayin gudanar da ayyuka.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta masana fasahar fata da kimiyyar sinadarai ta Nijeriya ta fitar ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa, Dr. Julius Putshaka, ya ce ya zama wajibi a yi nazari sosai kan illolin da ke tattare da irin wannan haɗewar na wasu hukumomi.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “rashin amincewar ƙungiyar masana fasahar fata da na kimiyyar sinadarai ta Nijeriya dangane da haɗewar waɗannan hukumomi ya samo asali ne daga damuwar da ke tattare da yiwuwar tafka asarar ƙwararrun masana saboda waɗannan cibiyoyi suna da hurumi daban-daban.
“A yayin da NILEST ke da alhakin gudanar da bincike tare da horar da ma’aikata a fannin fasahar fata da ƙirgi tare da samar da ɗaliban da za su yi wa masana’antar fata hidima da kuma wasu sassa da dama a wasu hukumomin gwamnati, Cibiyar NARICT a ɗaya ɓangaren kuma tana da alhakin gudanar da bincike a cikin albarkatun ƙasa domin samar da sinadarai da za a yi amfani da su wajen aikace-aikacen masana’antu.
“Dole ne a nanata cewa NILEST ta taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa ɓangarori masu muhimmanci a ɓangaren samar da fata da ƙirgi. Tare da cibiyoyi masu gudanar da ayyuka da kuma wasu da aka faɗaɗa ayyukan, ofisoshin cibiyar sun bazu a duk yankuna shida na siyasa na faɗin ƙasar, kuma ta kasance a matsayin jagora ga ‘yan kasuwa masu sana’ar dogaro da kai a masana’antar.
“Cibiyar ta horar da dubban ‘yan kasuwa da masu sana’o’in hannu a faɗin ƙasar nan tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyi daban-daban da gwamnatocin jihohi kuma har yanzu tana samar da ƙarin hanyoyin gudanar da irin waɗannan ayyuka.
“Yana da kyau a lura da irin tasirin da wannan cibiya za ta iya yi wajen samar da arziƙi da kuma musayar kuɗaɗen ƙasashen waje ga ƙasar nan ta hanyar samar da ingantattun fata da ƙirgi da za a iya fitar da su zuwa ƙasashen waje a manyan cibiyoyinta da ke Sakkwato, Kano, da Maiduguri.
Kamar dai yadda Cibiyar Fata da ta shahara a duniya ta Indiya take, NILEST ita ma tana ba da tallafin fasaha ta hanyar horar da darussan kan haɓaka ƙirƙira, yin samfuri tare da samarwa, bayar da shawarwari da tuntuɓa, shirya rahotannin yadda za a gudanar da ayyuka, da kula da inganci, tare da sauran ɗimbin ayyuka daban-daban.”
Hakazalika sun yi nuni da cewa, da irin nasarorin da aka samu da kuma tasirin da aka samu a ɓangarori da dama, haɗakar ka iya isar da saƙon koma baya a tsakanin masu ruwa da tsaki a masana’antar fata, musamman a wannan lokaci da NILEST ke aiwatar da manufofi da shirin gwamnatin tarayya kan harkokin fata da ƙirgi.
“Muna da ja kan cewa haɗewar na iya haifar da ruɗani wajen yanke hukunci, tare da kuma rage karsashi kan wasu batutuwa ko rashin samun daidaito wajen aiwatar da manufofin gwamnati, kawo cikas ga ayyukan da ake da su ko shirye-shirye a cikin masana’antar fata da NILEST ke aiwatarwa”, in ji sanarwar.
Kazalika sanarwar ta ce za a iya kuma samun karkatar ra’ayoyin masu ruwa da tsaki da kuma gurgunta ƙwazo da dabarun ƙwararru. A matsayin su na masu ruwa da tsaki a kan lamuran fata, kungiyar ta ce ta lura da cewa haɗewar waɗannan cibiyoyi, zai iya zama barazana ga masu ruwa da tsaki wanda zai haifar da gazawar cika alƙawuran alfanun da za a samu na irin wannan haɗakar.