Hukumar dake kula da kwallon kafa ta nahiyar Afirka ta CAF ta fitar da sunayen alkalan wasan da za su jagoranci yin alkalanci a gasar cin kofin nahiyar Afirka da kasar Cote d’Ivoir za ta karbi bakunci, amma babu alkalin ko guda daya daga Nijeriya.
Ana kallon Nijeriya a matsayin daya daga cikin manyan kasashen da suka fi shahara a harkar kwallon kafa a nahiyar Afirka kuma kasar da take da tasiri a nahiyar a fannoni da dama.
Sai dai rashin daukar wani daga cikin dubunnan alkalan wasan kasar nan wata alama ce wadda take nuna cewa akwai matsaloli birjik musamman a harkokin da suka shafi wasanni a kasar nan, kuma suke bukatar daukar mataki na gaggawa.
Dalilin da ya sa ba a dauki alkalin wasa daga Nijeriya ba
Cin Hanci Da Rashawa?
Cin hanci da rashawa dai yana daya daga cikin matsalolin da suka hana abubuwa da dama ci gaba a kasar nan ciki har da kwallon kafa inda ko a wasannin gasar firimiyar Nijeriya ma ana yawan korafi akan yadda ake samun matsalolin cin hanci da rashawa daga wajen kungiyoyi zuwa alkalan wasa.
Rashin Kayan Aiki Na Zamani
A yayin da aka samu ci gaba wajen saukakawa alkalan wasa ta hanyar na’urar taimaka musu wajen yanke hukunce-hukunce masu tsauri ta hanyar amfani da na’urar nan mai suna BAR, har yanzu a kasar nan ana fama da matsalolin BAR din domin hukumomi sun kasa yin abin da ya kamata wajen samar da na’urar a filayen wasannin dake fadin kasar nan.
Rashin Haska Gasar Firimiya Ta Nijeriya
Haska gasa yana taimaka wa wajen rage magudi, wanda kuma daman cin hanci da rashawa ne yake kawo magudin, saboda haka rashin haska wasannin gasar gaba daya shi ne yake sawa ake samun rashin tabbas a gasar, sannan suma alkalan wasan suna ganin duniya ba ta ganin su hakan yake sawa suke yin abin da suka ga dama a wajen yin alkalanci.
Hukumar kula da kwallon kafa ta Afirka, CAF ta sanya sunayen alkalan wasa 85 na sassa daban-daban, gabanin gasar cin kofin Afirka na shekara ta 2024 da kasar Cote d’Iboir za ta karbi bakunci.
Kamar yadda jerin sunayen ya fito a ranar Talata, alkalan wasan da suka fi yawa a cikin jerin sunayen sun fito ne daga kasashe biyu na Arewacin Afirka, wato Masar da Aljeriya.
A gasar da aka fafata wadda Kamaru ta karbi bakunci a baya, Samuel Pwadutakam ne dan Nijeriya daya tilo da aka saka cikin alkalan wasa 63 a gasar AFCON da ta gabata kuma shima ya je ne a matsayin mai jiran ko ta kwana.