Shahararren dan wasa Cristiano Ronaldo ya ci kwallo uku rigis, karo na biyu a gasar kwallon kafa ta Saudi Arabia, bayan da kungiyar Al Nassr ta ci Damak 3-0 ranar Asabar.
Tsohon dan wasan Real Madrid da Manchester United ya ci kwallo ukun tun kan zagaye na biyu a karawar kuma makonni biyu da suka wuce ya ci Al Wehda kwallo hudu rigis a babbar gasar ta Saudi Arabia.
Ronaldo ya fara zura kwallo a raga a bugun fenariti, bayan da Farouk Chafai ya taba kwallo da hannu a da’irar mai tsaron raga sannan ta biyu kuwa ya ci daga yadi na 20 da kafarsa ta hagu, sannan ya zura ta uku a raga saura minti daya su je hutun rabin lokaci.
Ronaldo ya ci kwallo uku rigis sau 44 a Real Madrid, wanda shi ne kan gaba a yawan ci wa kungiyar Santiago Bernabeu kwallaye a tarihi sannan dan kwallon tawagar Portugal din ya zura kwallaye uku rigis karo uku a sau biyu da ya yi wasa a Manchester United da cin wasu ukun rigis sau uku a Jubentus a kaka ukun da ya yi.
Ronaldo ya bar Manchester United tun kan fara gasar kofin duniya a Katar, wanda ya amince da komawa Saudi Arabia da buga wasa a cikin watan Janairu.