Kasashe hudu ne suka samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2026 da za a buga a kasashe uku da su ka hada da Canada da Medico da kuma Amurka, gasar cin kofin duniya ta 2026, wadda za a yi a ranar 11 ga Yuni zuwa 19 ga Yuli, 2026, ita ce gasar karo na 23 kuma za ta kasance gasar cin kofin duniya ta farko da kasashe uku za su karvi bakuncinta.
Wani gagarumin sauyi ga wannan gasa shi ne fadada yawan adadin kasashen da za su buga daga kasashe 32 zuwa 48, mahukuntan hukumar kwallon kafa ta FIFA ne su ka yanke wannan hukunci a bara, yayin da shekarun baya da su ka gabata kasashe 32 ne ke buga gasar Kofin Duniya amma yanzu FIFA ta kara kasashe 16.
- Jami’in Sin: Ba Za A Lamunci Ayyukan ‘Yan Aware Na “Ballewar Taiwan” Ta Ko Wace Hanya Ba
- Juma Bah: Balladolid Za Ta Kai Manchester City Kara Gaban Kotu
Tawagar farko da ta samu gurbin zuwa kasashen da ke karvar bakuncin ita ce Kasar Japan, Kasar Japan ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA a shekarar 2026, inda ta zama kasa ta farko a wajen kasashen da suka karvi bakuncin gasar.
Nasarar da suka yi a kan Bahrain da ci 2-0 a ranar Alhamis 20 ga watan Maris, ya sa su ka samu wannan nasara ta fara zuwa kofin Duniya na shekarar 2026, a ranar 24 ga Maris, 2025, New Zealand ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026, bayan da ta doke New Caledonia da ci 3-0, sai kasar Argentina wadda ta lashe kofin karshe na gasar Kofin Duniya da aka buga a kasar Katar a shekarar 2022, ita ma ta samu wannan nasara ta zuwa Kofin Duniya ne bayan ta doke kasar Brazil da ci 4-1 a Buines Aires.
Hakazalika kasar Iran ta samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026 a ranar Talata 25 ga Maris, 2025, sun samu hakan ne bayan da suka tashi kunnen doki 2-2 da kasar Uzbekistan a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Asiya, inda Mehdi Taremi ya zura wa Iran kwallayen biyu a wasan da suka tashi canjaras, wanda hakan ya ishe su hujja a wasan karshe.
Ya zuwa yanzu dai ga kasashen da suka samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026.
1. Japan(Asia). 2. New Zealand (Oceania). 3. Iran (Asia). 4. Argentina (Kudancin Amurka). 5. Kanada (Masu Masaukin Baki). 6. Meziko (Masu Masaukin Baki). 7. Amurka (Masu Masaukin Baki).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp