• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kofin Duniya: Kasar Saudiyya Za Ta Sassauta Dokar Hana Shan Giya A Wuraren Yawon Bude Ido 600

by Rabilu Sanusi Bena and Sulaiman
5 months ago
Kofin Duniya

Yayin da gasar kwallon kafa ta kofin Duniya ta shekarar 2034 ke kara matsowa, kasar Saudiyya za ta dage haramcin barasa da ta shafe shekaru da dama tanayi a wurare 600 da za a kebe a fadin kasar, a wani bangare na shirinta na kawo sauyi a shekarar 2030, da nufin bunkasa harkokin yawon bude ido da zuba jari a kasar.

 

A cewar Daily Mail, matakin da ba a taba daukar irinsa ba, zai ba da damar sayar da wasu zababbun abubuwan sha, wato giya da cider, a wuraren da aka ba da lasisi kamar su otal-otal masu alfarma, manyan wuraren shakatawa da manyan wuraren yawon bude ido, amma kuma za a haramta shan barasa a wuraren jama’a, gidaje masu zaman kansu, shagunan sayar da kayayyaki, da wuraren taron wasanni.

  • Shugaban Kasar Kenya: FOCAC Ya Samar Da Damammaki Ga Sin Da Afirka Wajen Inganta Hadin Kansu Da Samun Moriya Tare
  • Mummunan Hatsarin Mota Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 19 A Kogi

Wannan mataki da kasar ta dauka ya nuna karara yadda ta ke kokarin sauyawa daga ra’ayin yan mazan jiya da aka san masarautar da shi, wanda kuma ke nuna kokarin da Saudi Arabiya ke yi wajen janyo dimbin mutane masu yawon bude ido a kasar da wasu ke yiwa kallon masu tsatstsauran ra’ayi, a yayinda ta ke shirin karbar manyan wasanni na Duniya da suka hada da kofin Duniya na FIFA a 2034 da kuma Expo 2030.

 

LABARAI MASU NASABA

Barcelona Na Shirin Ɗauko Victor Osimhen Na Galatasaray

Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

A cewar jami’ai, za’a tsara yadda tsarin fitar da barasar zai kasance ta hanyar tabbatar da cewar an ba da horo ga masu sayar da ita da kuma basu takardar lasisin sayar da barasar. Hakazalika, za a tsaurara ka’idoji akan sayar da barasa a kasar, gwamnati ta jaddada cewa ana gabatar da sauye-sauyen ne cikin taka-tsantsan tare da kula da al’adun al’ummar kasar.

 

“Manufar ita ce, maraba da duniya ba tare da rasa asalin al’adu ba, sanya Saudiyya a matsayin mai ci gaba, duk da haka mai mutunta taswirar yawon shakatawa na duniya,” in ji hukumomin Saudiyya a cikin wata sanarwa.

 

Matakin ya zo ne a daidai lokacin da Saudiyya ke neman yin gogayya da kasashe makwabta kamar Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain, inda a bisa ka’ida ake samun barasa a wuraren yawon bude ido.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Barcelona Na Shirin Ɗauko Victor Osimhen Na Galatasaray
Wasanni

Barcelona Na Shirin Ɗauko Victor Osimhen Na Galatasaray

October 30, 2025
Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi
Wasanni

Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

October 28, 2025
El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid
Wasanni

El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid

October 26, 2025
Next Post
Sin Za Ta Harba Na’urar Binciken Samaniya Ta Tianwen-2

Sin Za Ta Harba Na’urar Binciken Samaniya Ta Tianwen-2

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

November 1, 2025
Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

November 1, 2025
An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

November 1, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu

Jerin Gwarazan Taurarinmu

November 1, 2025
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

October 31, 2025
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

October 31, 2025
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari

October 31, 2025
Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano

An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.