• English
  • Business News
Wednesday, May 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kofin Duniya Na 2034: Yadda Saudiyya Ta Fara Zama Jigo A Kwallon Kafa

by Abba Ibrahim Wada
2 years ago
in Wasanni
0
Saudiyya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Samun damar karbar bakuncin gasar cin kofin Duniya a Saudiyya, abu ne wanda bai zo da mamaki ba kuma an dade ana sa ran zuwansa, duba da yadda kawo yanzu kasar ke zuba jari a fagen wasanni a shekarun baya-bayan nan.

To amma duk mutumin da ke la’akari kan yadda Saudiyya ta gudanar da gagarumin sauye-sauye – a fannin wasannin kwallon golf ta hanyar shirya gasannin wasan, ko yadda kasar ta mamaye karbar bakuncin manyan gasannin damben zamani, ko kuma yadda ta zuba jari a fagen kasuwancin ‘yan wasan kwallon kafa – hakan ba zai zama abin mamaki ba.

  • Chelsea Ta Lallasa Tottenham Har Gida Da Ci 4-1
  • Maddison Ba Zai Buga Wasansu Da Liverpool Ba Saboda Raunin Da Ya Samu

Yawan ganawa da shugaban FIFA, Gianni Infantino ke yi da Yariman Saudiyya a shekarun baya-bayan nan, ka iya zama wata alama ta yadda kasar ke kara zama mai karfin fada-a-ji a fagen wasanni.

To amma, duk da matsayin kasar a fagen wasanni, batun daukar nauyin gasar Kofin Dunya a Saudiyya zai bai wa mutane da dama mamaki domin a yanzu da kasar ke da kusan tabbacin damar daukar nauyin gasar nan da shekara 11 masu zuwa, kasar za ta iya fuskantar ce-ce-ku-ce fiye da yadda Katar ta fuskanta a shekarar da ta gabata.

Kama daga matsalolin da suka shafi tauye hakkin bil-adama, da yadda FIFA ke tafiyar da batun takarar daukar nauyin gasar, ga kuma batun sauya lokacin gasar, da kuma walwalar ‘yan wasa sakamakon yiwuwar gudanar da gasar a lokacin hunturu, saboda matsancin zafi da ake fuskanta a lokacin bazara a kasar.

Labarai Masu Nasaba

Abinda Ya Kamata Kusani Akan Wasan El Classico Na Yau

Barin Liverpool Ita Ce Shawara Mafi Wahala Da Na Taɓa Yankewa A Rayuwata -Alexander 

Ganin yadda aka fadada kasashen da za su halarci gasar zuwa 48, yawan sauye-sauyen da kasar za ta yi sun zarta na Katar, sakamakon gina muhimman wuraren da ake bukata, na kara saka shakku game da yadda kasar za ta tunkari wannan gagarumin sauyi.

Masu suka da dama na kallon hakan a matsayin nuna sha’awa a ‘fagen wasanni’ ga kasar da ke zama babbar mai fitar da man fetur a duniya haka kuma akwai fargabar tauye hakkin mata, da haramta neman jinsi, da takaita ‘yancin fadar albarkacin baki, da ci gaba da yanke hukuncin kisa, ga batun zargin kisan fitaccen dan jaridar nan Jamal Khashoggi a shekarar 2018, tare da zargin hannun kasar a yakin Yemen.

To sai dai hukumomin Saudiyya sun sha musanta haka, suna masu cewa bukatarsu ta daukar nauyin gasar, zai taimaka wajen zamanantar da kasar, wajen inganta harkokin wasanni, tare da karfafa wa matasa gwiwwa, bunkasa yawon bude-ido, da bunkansa hanyar samun kudin shiga ga kasar, kafin karewar man fetur, tare kuma da hada kan kasashen duniya.

Sun nuna irin ci gaban da kasar ta samu a fagen kwallon kafar mata alal misali, suna masu cewa wannan wata dama ce ta bunkasa harkokin wasannin kwallon kafa, bayan samun nasarar daukar nauyin wasu gasanni.

Da karfafa gasar kwallon kafar kasar ta ‘Saudi Pro League’ da sayen kungiyar Newcastle United, da kuma shirin kasar na daukar nauyin gasar Kofin Duniya ta kungiyoyi a lokacin hunturu, ga kuma daukar nauyin gasar kasashen Asiya ta AFC a shekarar 2027.

To sai dai yayin da aka fi samun sha’awar kwallon kafa a Saudiyya fiye da Katar, mutanen da ke halartar kallon gasar Pro League sun ragu a wannan kakar hakan ya sa ake ganin ko ma mene ne manufar jagororin kasar, kasancewarta kasa daya tilo da ke takarar karbar bakuncin gasar a 2034, zai rage wa FIFA wahalar yanke hukunci.

Sanarwar FIFA na gabatar da bukatar karbar bakuncin gasar ta 2034 a farkon wannan wata ya zo wa mutane da ba-zata, kasancewar FIFA ta kayyade cewa dole kasar da za ta yi takarar ta fito daga yankin Asiya ko Oceania, tare da bayar da wa’adin kwana 26 ga masu takarar donsu bayyana sha’awarsu.

Daga nan – cikin ‘yan mintuna – Saudiyya ta bayyana sha’awarta a hukumance, inda kuma hukumar kwallon kafar yankin Asiya ta nuna goyon bayanta kan matakin na Saudiyya.

A wani mataki kuma da wasu ke gani kamar alfarma aka yi wa Saudiyya, FIFA ta sasauta dokarta kan gina sabbin filayen wasa, inda a yanzu ake bukatar masu neman daukar nauyin gasar su kasance suna da ginannu filayen wasa hudu (a maimakon dokar yanzu ta filaye bakwai).

A yanzu da Australiya ta dauki matakin janyewa daga takarar, ana ganin ta yi hakan ne saboda ta san ba za ta iya ja da Saudiyya ba a wannan takara kasancewar karfin tattalin arzikin nasu ba daya bane.

A watan Maris ne kungiyar shirya gasar kwallon kafa ta duniya – wadda ke wakiltar gasar lig na kasashe a duniya – ta bayyana ‘damuwarta kan ikirarin da ta yi na cewa FIFA ba ta tuntubeta ba kan sauya lokacin wasan kwallon kafa a duniya ciki har da kara yawan kasashen da za su halarci gasar Kofin Duniya ta 2026.

Haka kuma kungiyar kare hakkin bil-adama ta Human Rights Watch ta zargi FIFA da yin watsi da dokokinta, tana mai cewa abin kunya ne ga FIFA idan har ta bai wa Saudiyya damar daukar nauyin gasar kofin duniya ta 2034, kasancewarta mai tarihin tauye hakkin bil-adama da rashin bayar da dama ga kungiyoyin kare hakkin dan’Adam don gudanar da ayyukansu, kuma tabbas hakan na saka shakku kan kudurin FIFA na tabbatar da ‘yancin dan’Adam”.

To sai dai FIFA ta ki cewa komai kan batun, to amma ta dage cewa ‘yancin dan’Adam na daga cikin manyan ka’idoji neman daukar nauyin bakuncin gasar kuma Saudiyya za ta kasance daya daga cikin kasashen da daukar nauyin babbar gasar duniya ke janyo ce-ce-ku-ce a baya-bayan nan.

Alakar neman jinsi haramun ne a Morocco, wadda ke daya daga cikin kasashen da za su karbi bakuncin gasar 2030, kamar yadda yake a Katar, haka kuma batun yake a Saudiyya.

Masu goyon bayan auren jinsi, wadanda suka ce ba sa jin za su samu kariya a gasar Kofin Duniyar da ya gabata, a yanzu za su ji ba lallai su halarci gasar biyu masu zuwa ba.

Shin za a iya samun zanga-zangar ‘yan wasa kamar yadda aka gani a Katar, lokacin da tawagar Jamus ta nuna goyon bayanta ga masu neman jinsi?, Shin wadanne kasashe ne za su kaurace wa gasar?

Abin da ke bayyane a fili shi ne yadda ake samun sauyi ta fuska wasanni a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya domin a baya in aka ce karamar kasa irin Katar da makobciyarta Saudiyya za su iya daukar nauyin bakuncin gasar Kofin Duniya har guda biyu cikin shekara 12, mutane da dama za su yi mamakin hakan.

To amma idan aka yi la’akari da dimbin arzikin da kasashen ke da shi da yadda salon FIFA ya sauya musamman karkashin jagorancin shugabanta Gianni Infantino, hakan ba abin mamaki bane.

A yanzu ‘yan kasar Saudiyya, za su ci gaba da kare kansu kan abin da suke gani a matsayin munafurci, suna nuni da huldar kasuwanci da mafi yawan kasashen Yamma ke jin dadin kullawa da su.

Suna masu cewa kasashen na jahiltar Saudiyya, kamar yadda tauraron damben boding, Tyson Fury ya fada a baya-bayan nan, bayan ya yi wasa a Birnin Riyadh, inda ya ce bai kamata mutane su yanke wa kasar hukunci kafin su ziyarce ta ba.

Hukumomin kasar za su kwatanta da Katar, wadda duk kuwa da sukar da ta sha, ta samu damar daukar nauyin gasar da mutane da dama suka kalla a matsayin nasara.

Amma kuma ko ma dai mene ne, a yanzu FIFA da Hukumomin Saudiyya na da shekara 11 domin su nuna wa masu shakku cewa za su iya shirya gasar duk da irin kalubalen da za su fuskanta.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: ArgentinaKofin DuniyaSaudiyya
ShareTweetSendShare
Previous Post

An Yi Taron Karawa Juna Sani Tsakanin Sin Da Amurka Kan Shari’a Da Hakkin Dan Adam

Next Post

Kwamitin Sulhun MDD Ya Kira Taron Gaggawa Kan Yanayin Da Palastinu Da Isra’ila Ke Ciki

Related

Abinda Ya Kamata Kusani Akan Wasan El Classico Na Yau
Wasanni

Abinda Ya Kamata Kusani Akan Wasan El Classico Na Yau

3 days ago
Barin Liverpool Ita Ce Shawara Mafi Wahala Da Na Taɓa Yankewa A Rayuwata -Alexander 
Wasanni

Barin Liverpool Ita Ce Shawara Mafi Wahala Da Na Taɓa Yankewa A Rayuwata -Alexander 

3 days ago
Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa
Manyan Labarai

Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa

6 days ago
Zamalek Ta Sallami Tsohon Kocin Super Eagles, Peseiro
Wasanni

Zamalek Ta Sallami Tsohon Kocin Super Eagles, Peseiro

6 days ago
PSG Ta Yi Waje Rod Da Arsenal A Gasar Zakarun Turai 
Wasanni

PSG Ta Yi Waje Rod Da Arsenal A Gasar Zakarun Turai 

7 days ago
UEFA: Inter Milan Ta Yi Wa Barcelona Kancal
Wasanni

UEFA: An Kai Ruwa Rana Yayin Da Inter Ta Koro Barcelona Gida

1 week ago
Next Post
Mdd

Kwamitin Sulhun MDD Ya Kira Taron Gaggawa Kan Yanayin Da Palastinu Da Isra’ila Ke Ciki

LABARAI MASU NASABA

Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha

Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha

May 14, 2025
Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin

Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin

May 14, 2025
‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 239, Sun Ƙwato Makamai Da Alburusai A Kogi

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 239, Sun Ƙwato Makamai Da Alburusai A Kogi

May 14, 2025
Dakarun Soji Sun Daƙile Wani Sabon Harin ISWAP A Dikwa

Dakarun Soji Sun Daƙile Wani Sabon Harin ISWAP A Dikwa

May 14, 2025
Sojoji 20 Sun Ɓace Bayan Harin Da ISWAP Suka Kai Marte

Sojoji 20 Sun Ɓace Bayan Harin Da ISWAP Suka Kai Marte

May 14, 2025
Ko Kanawa Za Su Yafe Wa Ganduje?

Kotu Ta Ce Za A Ci Gaba Da Shari’ar Ganduje Kan Zargin Aikata Rashawa A Kano

May 14, 2025
Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

May 13, 2025
Tsaro: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci 140 Ga Jami’an Tsaro A Zamfara 

Tsaro: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci 140 Ga Jami’an Tsaro A Zamfara 

May 13, 2025
Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

May 13, 2025
Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe

Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe

May 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.