• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kogin Kumadugu Ya Yi Ambaliya Karon Farko Cikin Shekara 100 A Yobe

by Muhammad Maitela
3 years ago
Kumadugu

Al’ummar jihar Yobe, sun bayyana cewa sama da shekara 100 ba a taba ganin makamancin ibtila’in ambaliyar ruwa daga kogin Kumadugu ba da ya mamaye dubban gidaje da amfanin gonakin jama’a.

Wani dattijo mai shekara 78 a garin Gwio Kura da ke karamar hukumar Bade (Gashuwa), yankin Gwio Kura, Baani Ari Kolo, ya bayyana cewa duk dan shekara 100 ba shi da masaniyar malalar ruwan Kogin Kumadugu zuwa garin Gwio Kura da kauyukan da ke makobtaka da ita.

Ya ce a wannan shekara sun fuskanci mummunar ambaliyar ruwan Kogin wanda ya lalata amfanin gonakin dubban jama’a tare da ruguza gidajensu.

Kumadugu

“Bana ina da shekara 78 a duniya, kuma ni haifaffen garin Gwio Kura ne da ke karamar hukumar Bade. Bana Allah ya jarabce mu da ibtila’in ambaliyar ruwan Kogin Kumadugu wanda ya mamaye garuruwanmu da gonakinmu; sannan duk dan shekara 100 ba zai gaya maka cewa ya san ruwan Kogin ya na zuwa wadannan garuruwa namu ba. Saboda haka muna kira ga gwamnatocin Tarayya da ta jihar Yobe su kawo mana daukin gaggawa, hadi da Kungiyoyin jinkai.” In ji shi.

LABARAI MASU NASABA

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

Al’ummar jihar Yobe sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta kawo musu daukin gaggawa saboda yadda suke ci gaba da fuskantar mummunan ambaliyar ruwan da ta mamaye garuruwansu tare da amfanin gonakin da suka noma a daminar bana.

Haka kuma, sun nuna fargabar barkewar yunwa da fatara sakamakon yadda ambaliyar ruwan ta yi musu kwab-daya ta yadda ba su a tsuntsu kuma ba su ba tarko- yayin da ambaliyar ruwan ta ruguza gidaje tare da lakume amfanin gonakin da suka noma.

  • Firaministan Habasha Ya Kaddamar Da Dakin Adana Kayan Kimiyya Da Fasaha Da Kasar Sin Ta Samar
  • Bukatar Samar Wa Kotunan Korafe-korafen Zabe Kudaden Gudanarwa

Wannan mummunan ambaliyar ruwan ta faru ne sakamakon tumbatsar da Kogin Kumadugu (Riber Yobe) ya yi inda ya malala ruwan tare da mamaye garuruwa da daman gaske hadi da barnata amfanin gonakin dubban jama’ar jihar Yobe.

Wanda ya tilasta jama’a fitowa fili tare da neman gudumawar gaggawa daga Gwamnonin Tarayya da sauran kungiyoyin jinkai a ciki da wajen kasar nan. Kamar yadda aka sani, Kogin Kumadugu (Riber Yobe) ya na daga cikin manyan koguna a Yammacin Afrika wanda ya fada Tafkin Chadi.

Kogi ne wanda ruwan sa ke fitowa daga Kogin Hadeja, Kogin Jama’are hadi da Kumadugu Gana, da wasu Dama-damai da ke antayo ruwansu zuwa kogin, sannan daga cikin manyan garuruwan da suke zaune kan gabar Kogin sun hada da Gashuwa, Gaidam da Damasak a Nijeriya, sai garin Diffa a Nijar.

A wannan shekara, Kogin Kumadugu ya yi cika ya batse tare da tumbatsar da ta haifar da mummunan ambaliyar ruwan da ta shafe wasu garuruwa da dama a jihar Yobe, musamman a kananan hukumomin Bade (Gashu’a) da Jakusko- uwa uba garin Gashuwa da kauyukanta, wanda baya ga mamaye kauyukan kuma ya yi wa garin Gashuwa kawanya da mamaye unguwannin Katuzu, Abujan Amarebda wani yanki na Zango da Unguwan Lawan.

A unguwar Abujan Amare, ambaliyar ruwan ya rusa sama da gidaje 200, haka kuma ruwan ya rusa fiye da wannan adadin a unguwar Katuzu, tare da mamaye Kasuwar Danyen Kaya, Katuzu Primary, Keasawa Primary da shagunan jama’a da ke bakin Tashar Kuka, duk a cikin garin Gashuwa. Yayin da ambaliyar ruwan ta shafi baki dayan gundumomi 10 da ke karamar hukumar Bade, wanda na baya -bayan ne su ne garuruwan Gasima da Dagona da ambaliyar ruwan ta mamaye baki daya.

A hannu guda kuma, ambaliyar ruwan ta yi wa kauyuka da garuruwa da daman gaske dukan a kawo wuka a karamar hukumar Jakusko; ta rushe gidajen jama’a tare da lamushe amfanin gonakinsu- daga ciki akwai garin Girgir, Katamma, Amshi, Guyik, Muguram, Jaba, Jakusko, Dumbari, Gwayo, Dukorel, Lafiya, Bayam, Buduwa, Saminaka, Garin Saje, Dachiya, Zabudum da sauransu. Sauran sun hada da Gasamu, Garin-Mallam, Gamajan, Sabon Sara, Garin Kunu, Kurkushe, Adiya, Damasa, Yim, Kazir, Gafala, Arfani, Kambawo da garin Daklam duk a karamar hukumar Jakusko da ke jihar Yobe.

Bugu da kari kuma, ambaliyar ruwan ta kai Kwanan Koromari (tsakanin Gashu’a zuwa Bayamari) a karamar hukumar Bursari yayin da take barazana ga kauyuka 10 da ke yankin, wadanda suka hada da Girim Bade, Girim Kanuri, Gilbasu Yamma, Gilbasau Tsakiya, Gilbasau Gabar, Dapso, Garin Kabaju, Guba, Kormari da Kurnawa.

A hannu guda kuma, wannan mummunan ambaliyar ruwan ta shamakance wasu kauyukan da ba za a iya shiga ko fita daga cikinsu ba face sai ta hanyar amfani da jiragen kwale-kwale, wanda suka kunshi Kirikasamma, Awakurari, Damakarwa, Lawan kaltume, Dawai, Buwa, Bulakuwa, Bulanguwa, Goyeri, Daudari, Maladari, Malumma kawuwa, Jajeri, Guluri, Mallari, Karabiri, Kesala, Dalari, Darwo Shilandi, Darwo mariri, Darwo Kakanari da kauyen Darwo Lambowu a karamar hukumar Gaidam.

Wadannan jama’a wadanda ibtila’in ya shafa, suna ci gaba da bayyana bacin ransu bisa ga halin ko-in-kula da gwamnatocin Tarayya da na jihar ke nuna musu kan halin da suke ciki.

Alhaji Kanzi, Mai Unguwar Abujan Amare da ke cikin garin Gashuwa, ya ce al’ummar sa suna cikin mawuyacin hali, “Yau sama da kwana 12 muna bakin jingar tare ruwan nan (babu dare babu rana), amma har yanzu ba mu taba samun tallafin gwamnati ba. Hana rantsuwa Shugaban karamar hukumar Bade ya kawo mana gudumawar 20,000, sai Sarkin Bade, ya ba mu buhun garin-kwaki biyu da fatun buhuna 500.Wannan shi ne iyakacin tallafin da muka samu a wannan lokacin.

“Har wala yau, ambaliyar ruwan ta katse manyan hanyoyin jihar, hanyar da ta tashi daga Gashu’a zuwa Bayamari ta shiga Damaturu, da wadda ta tashi daga Gashu’a zuwa Jakusko ta wuce Potiskum zuwa Damaturu, dole sai ta jiragen kwale-kwale al’amarin da ya tilasta jama’a da sauran ma’aikata da ‘yan kasuwa a yankin zagayawa jihar Jigawa sannan su shiga Damaturu.

Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar Yobe (SEMA), Dakta Mohammed Goje ya shaida wa wakilinmu a jihar cewa ambaliyar ta shafi kimanin magidanta 31,000 a cikin garuruwa da kauyuka 255 a kananan hukumomin 17 a jihar Yobe, sannan kuma ta tilasta wa sama da mutane 6,592 zama a sansanin yan gudun hijira, sakamakon rugujewar gidajensu.

Dakta Goje ya kara da cewa, kananan hukumomin Gujba, Gulani, Jakusko,Tarmuwa, Geidam da Bade su ne suka fi sauran fuskantar mummunan kalubalen ambaliyar ruwan, wanda sama da shekara 50 ba a ga irinsa ba a yankin.

 Baya ga rasa rayuka da raunuka ga kimanin mutane sama da 200 hadi da lalata amfanin gonakin dubban jama’a.

A nashi bangaren, Shugaban karamar hukumar Bade, Hon. Sanda Kara-Bade ya bayyana cewa, ambaliyar ruwan ta tagayyara rayuwar jama’a, bsaboda yadda ta rushe gidajensu tare da barnata amfanin gonakin da suka noma. Al’amarin da ya ce dole sai an tashi tsaye wajen tunkarar wannan ibtila’in.

Ya ce, “Saboda haka muna mika sakon godiyarmu ga hukumar SEMA dangane da tallafin da suka bai wa jama’ar da wannan ibtila’in ya shafa. Amma muna kara mika kokon baranmu al’ummarmu ga Gwamnatin Tarayya da ta jihar Yobe su kara kaimi tare da tallafa wa jama’a saboda ana cikin mawuyacin halin gaba kura ba ya sayaki ambaliyar ruwan ta lalata gidaje da gonakin jama’a.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum
Manyan Labarai

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”
Labarai

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano
Manyan Labarai

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Next Post
Rundunar ‘Yansanda Ta Kame Mutum 44 Bisa Zargin Aikata Ba Daidai Ba A Adamawa

Rundunar 'Yansanda Ta Kame Mutum 44 Bisa Zargin Aikata Ba Daidai Ba A Adamawa

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

October 26, 2025
Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

October 26, 2025
Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.