Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa yana ganin a kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr ta kasar Saudiyya zai yi ritaya daga buga kwallo a duniya baki daya. A ranar 30 ga watan Disamban 2022 ne kyaftin din tawagar kasar Portugal.
din, Cristiano Ronaldo ya koma buga wasa a kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya kuma ya koma kungiyar ne a kan farashin Fam miliyan 200 duk shekara, wanda shi ne albashi mafi tsoka a kwallon kafa.
- Ronaldo Ya Jefa Kwallo Biyu Yayin Da Portugal Ta Lallasa Bosnia Da Ci 5-0
- Ronaldo Ya Fashe Da Kuka Bayan Rashin Nasara A Wasan Ƙarshe
Sai dai tun bayan komawarsa Saudiya masu sharhi a kan harkar suke ci gaba da tattauna nasarar da ya samu da akasin haka inda a ranar Asabar ne 17 ga Agusta ce Al-Hilal ta lallasa Al-Nassr da ci hudu da 1 a wasan Saudi Super Cup.
Ronaldo ne ya fara zuwa kwallo a wasan bayan minti 44, inda magoya bayan kungiyar suka fara murna, kafin daga bisa murnar ta koma ciki kuma hakan na zuwa ne bayan a ranar 1 ga Yuni, Al-Hilal din ta doke Al-Nassr a wasan Kofin Kings Cup, inda Al-Hilal ta yi nasara a bugun fanareti bayan an tashi canjaras.
Bayan an tashi wasan ne fitaccen dan wasan ya fashe da kuka, inda abokan wasansa suka taru a kansa suna ba shi hakuri haka kuma na biyu Al-Nassr ta kare a gasar Sausi Pro League a kakar bara kuma har yanzu kofin da ya ci tun zuwansa kungiyar ita ce Kofin Arab Club ta kakar bara.
Ganin yadda Al-Hilal ke ci gaba da kaka-gida a wasan kwallon Saudiyyar ce ya sa ake ganin shin akwai amfanin da zuwan Ronaldo ya yi wa Al-Nassr?
A bangaren zura kwallaye ba a cewa komai, domin a kakar bara ya kafa tarihin cin kwallaye a gasar, inda ya zura kwallo 35 a kaka daya, inda ya karya tarihin Abderrazak Hamdallah, wanda ya taba zura kwallo 34 a kakar 2028-2019. Zuwa yanzu, dan wasan na zura kwallo 67, ya taimaka an ci kwallo 16 a wasa 73 da ya buga wa kungiyar ta Al-Nassr. Ke nan za a iya cewa a
matakinsa da dan wasa, ya ci kwallaye, kuma ya nuna bajinta, sai dai duk kungiyar da ya buga wa kwallo ya lashe kofi, ciki har da Sporting CP, inda ya faro a Portugal.
Sai dai yadda Al-Nassr din ba ta lashe kofuna sosai, sai wasu ke diga alamar tambaya a kan nasarar da ya samu a kungiyar domin kafin komawarsa Al-Nassr, Ronaldo ya lashe kofuna da dama a kungiyoyin da ya buga wasa, kamar Manchester United, da Real Madrid, inda ya fi lashe kofuna.
Sannan ya lashe kofuna a kungiyar Jubentus, inda ya je kafin ya koma Saudiyya. Babban dalilin da ya sa kungiyar Al-Nassr ta dauki dan wasa Ronaldo shi ne cin kofi sannan zuwansa zai taimaka wajen ganin wasu ‘yan wasan sun shiga kungiyar, kamar yadda daga baya irinsu Sadio Mane da Aled Telles suka bishi kungiyar.
Sai dai kuma kungiyar Al-Hilal tana da matukar tasiri a kwallon kafa a Saudiyya, sannan ta dauki zakakuran ‘yan wasa daga Nahiyar Turai sama da wadanda Al-Nassr ta dauka wanda hakan ya sa take ci gaba da jan zarenta.
Sai dai har yanzu akwai jan aiki a gaban kungiyar Al-Nassr wajen ganin ta sha gaban kungiyar Al-Hilal musamman lashe kofunan kasar Saudiyya tare kuma da mamaye gasar kasar Saudiyya kamar yadda Al-Hilar ta yi.